Zan Murkushe Duk Wani Dan Ta’adda A Zamfara- Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin Gusau na bayyana cewar Sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, Yakubu Elkana, ya ja kunnen shu’uman ‘yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara inda yace ko dai su zubar da makamansu ko kuma su fuskanci hukunci mai muni. Kwamishina Elkana ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Laraba, inda ya hori ‘yan bindiga suyi gaggawar baiwa gwamnatin jihar hadin kai wurin samar da zaman lafiya ko kuma su ga aiki da cikawa. Tsarin aikina cikin dabara zai fara, zamu yi…

Read More

Adamawa: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Cafke Shahararrun ‘Yan Bindiga 14

Rudunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da mutane sha hudu wadanda ake zargi masu yin garkuwa da mutane ne a wurare daban daban dake fadin jahar. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yola. D S P Suleiman Nguroje yace an kama mutanen ne a maboyarsu dake wurare daban daban karkashi jagorancin Jami an tsaro na SIB dake jahar ta Adamawa. Sanarwa taci gaba da cewa mutanen da ake zargin sun…

Read More

Rashin Hukunta Masu Laifi Ne Silar Wanzuwar Ta’addanci A Najeriya – Jakadan Hayin Banki

An bayyana cewar rashin daukar matakin hukunta masu aikata manyan laifuka na ta’addanci a Najeriya shine dalilin da ya sanya har yanzu ayyukan ta’addanci suka ki karewa a Najeriya. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani Basarake a Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba Jakadan Hayin Banki a lokacin da yake tsokaci dangane da kisan matafiya sama da 30 da wasu tsagerun matasa suka yi a Jos babban birnin Jihar Filato. Gambo Abba ya bada misali da abin da ya faru a shekarun baya na rikicin Zangon Kataf, inda…

Read More

Bamu Goyi Bayan Yin Afuwa Ga Tubabbun Boko Haram Ba – Dattawan Arewa

Kungiyar tuntuba ta Dattawan Arewa Arewa Consultative Forum, ta yi watsi da maganar yafewa yan ta’addan Boko Haram da suke mika wuya ga gwamnati da kuma sakinsu, kamar yadda gwamnati ta kuduri aniyar yi. Shugaban kungiyar na kasa, Cif Audu Ogbeh, ya ce wajibi ne a hukunta yan ta’addan kan laifukan da suka aikata kan yan Najeriya, cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba. Ogbeh, wanda tsohon Ministan noma ne, ya bayyana hakan a jawabin da ya rattafa hannu kuma kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe, ya sake a Kaduna ranar…

Read More

Katsina: Kowa Ya Nemi Makami Don Kare Kai – Masari

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya bu?aci mazauna garuruwan da ‘yan bindiga ke yawan kai wa hare-hare da su nemi makamai don kare kan su daga hare-haren. Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da ya kai ziyarar jaje a ?aramar Hukumar Jibia ga iyalan mutum 10 da jami’an hukumar kwastan suka kashe a makon da ya gabata. Katsina na cikin jihohin da ‘yan bindiga suka fi kashewa tare da yin garkuwa da mutane a arewa maso yamnmacin Najeriya. Ranar…

Read More

Zamfara: ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Daliban Kwalejin Noma Sun Nemi Miliyan 350

Yan bindigan da suka sace malamai da ?alibai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura, jihar Zamfara, sun nemi a basu miliyan N350m ku?in fansa. Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntu?e shi ta wayar salula. Yace yan bindiga sun nemi a ba su miliyan N350m ku?in fansar mutum 20 dake hannun su a yanzun sannan su sako su. Mainasara yace: “Sun fa?a mun cewa sai an basu kudin da suka bukata kafin su sako ?alibai da malaman da…

Read More

Matsalar Tsaro: Buhari Zai Gana Da Shugabannin Tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro a fadarsa a ranar Alhamis kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito. Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce Buhari wanda ya dawo daga London a ranar Juma’a zai gana da shugabannin tsaron ne domin tsara tsare-tsaren kawo ?arshen ?alubalen tsaro da ke gabansu. Sanarwar ta ce jami’an tsaron ?asar sun ?ara ?aimi wajen ya?i da masu tayar da ?ayar baya da ?an fashin daji da sauran masu aikata laifuka da suka addabi ?asar wa?anda hakan ke sa suke mi?a…

Read More

‘Yan Bindiga Sun Yi Mummunan Ta’adi A Kudancin Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana adadin wasu mutane masu yawa sun rasa ransu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Gora Gida, karamar hukumar Zangon Kataf, dake kudancin jihar Kaduna a karshen mako. Da yake magana da manema labarai Hakimin Gora, Mr Elias Gora, yace yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi. Ya kara da cewa wata mata ta samu raunin harbin bindiga sannan kuma maharan sun kona mota guda ?aya. Mr. Gora ya kara da cewa mutum biyu…

Read More

Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Kwalejin Noma Bakura Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa an sace ?alibai da dama da malamai a Kwalejin Noma da ke garin Bakura. Mataimakin rijistara na kwalejin Malam Aliyu Bakura, ya tabbatar wa da BBC wannan labari. Ya ce ‘yan Bindigar sun kashe mutum hu?u da suka ha?a da ?an sanda ?aya da masu gadi uku. Ya ce “a jiya Lahadi da daddare wajen ?arfe 10 suka shiga suka yi ta harbe-harbe suka kwashe ?alibai 15 da kuma wani malami da matarsa da ?a?ansa biyu,” a cewarsa. Malam Aliyu ya ce maharan suna…

Read More

Miyyeti Allah Ta Yi Kiran Gaggawar Kama Wadanda Suka Yi Kisan Jos

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu ‘yan ta’adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, a ranar Asabar inda suka karkashe Mutane kimanin 30. ?ungiyar ta Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos ya fitar, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba. “Harin na kwanton baunar da ya faru da misalin karfe 10:00 na safe, ya kuma raunata matafiya…

Read More

Kungiyar Kiristoci Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Musulmi A Jos

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Filato, a ranar Lahadin da ta gabata ta yi Allah wadai da kisan wasu matafiya musulmai 25 a hanyar Rukuba, a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar. Rev. Fr. Polycarp Lubo, shugaban CAN a jihar, ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka aikata danyen aikin, domin hukunta su kamar yadda doka ta tanada. Wasu fusatattun matasa da ake zargin ‘yan ?abilar Irigwe ne suka kai hari kan motocin bas guda biyar dauke da matafiya Musulmai sama da 90, suka kashe…

Read More

Kisan Jos: Mun Zuba Ido Muga Matakin Da Gwamnati Za Ta Dauka – Jingir

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Shiekh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga Musulmi a fadin kasar nan da su kwantar da hankalinsu bayan kisan matafiya musulmai da aka yi a Jos ranar Asabar. Ya yi wannan kira ne a wata hira da manema labarai ranar Lahadi a Jos, dangane da kisan gilla da wasu Matasan Kiristoci suka yi wa Musulmi matafiya har su 33 a garin Jos. Ya ce duk da kisan yana da zafi da bakin ciki, amma bai kamata mutane…

Read More

Kisan Matafiya: A Tsawaita Dokar Hana Walwala A Jos

Rahotanni daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Gwamnatin Jihar Filato ta ce dokar hana fitar da ta saka ta zama ta zaman gida baki ?aya biyo bayan kashe matafiya Musulmai da “matasan ?abilar Irigwe” suka yi a Jos, babban birnin jihar. Tun farko an ?a?aba dokar hana fitar ce daga 6:00 na yamma zuwa 60:00 na safe a ?ananan hukumomin Jos Ta Kudu da Jos ta Arewa da kuma Bassa. Amma ?arin ya shafi Jos ta Arewa ne ka?ai. A ranar Asabar ne matasan suka tare matafiyan…

Read More

Buhari Ya Bada Umarnin Kamo Matasan Da Suka Yi Wa Matafiya Kisan Gilla A Jos

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su tabbata sun kamo duk wa?anda ke da hannu a kasar matafiya da matsasa ?auke da makamai suka yi Jos, Jihar Filato. Kakakin fadar shugaban kasa, Garba shehu ya fitar da wannan sanarwa da ya ke kunshe da sakon shugaban kasa. Sanarwar ta cigaba da cewa shugaba Buhari ya ce gwamnati ba za ta sa ka ido kawai wasu gungun b?ata gari su riki yin abinda suka dama kuma a kyale su ba. ” Wannan hari ba rikin Makiyaya da Manoma bane,…

Read More

Filato: Matasan Birom Sun Hallaka Matafiya Sama Da 20 A Jos

Wasu matasa da ake kyautata zaton ‘yan ?abilar Birom ne ?auke da muggan makamai sun tare wasu manyan motocin bas mai cin mutum 18 a hanyar Jos zuwa Zaria inda suka far musu suka kashe akalla mutum sama da 20, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito. Daily Nigerian wanda ta ce wakilinta ya ziyarci wannan wuri bayan wannan mummunar abu ya auku. Ya ce matafiyan na dawowa daga taron murnar shiga sabuwar shekarar musulunci wanda aka yi a garin Bauchi bisa gayyatar Sheikh Dahiru Bauchi, kamar yadda Ibrahim wanda…

Read More

Gwamnatin Buhari Ta Gaza Wajen Samar Da Tsaro – ?ungiyar Kare Hakkin Bil-Adama

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana takaicin ta game da gazawar gwamnatin tarayyar Najeriya na samarwa jama’ar kasar tsaron da ya kamata. Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani rahoto da ta fitar, game da yanayin da tsaro ke ciki a Najeriyar. A cewar Amnesty International cikin wata guda kadai an kashe mutane 112 a rikice-rikicen da aka samu a jihohin Kaduna da Plateau a Najeriyar. Kungiyar cikin rahoton da ta fitar ta ce baya ga mutanen da suka hallaka dalilin rikice-rikicen, masu garkuwa da mutane…

Read More

Zamfara: Farmakin Soji Ya Bar Tulin Gawawwakin ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar wani harin ha?in guiwa da sojojin sama da na kasa suka kai dajin Sabubu dake jihar Zamfara karkashin Operation Hadarin Daji ya sa an hallaka yan bindiga da dama. An ruwaito cewa an gano manyan yan ta’adda na ciki da wajen jihar sun taru a wani wuri da ake zargin ma?oyar kasurgumin ?an bindiga, Halilu Tubali ne a arewacin dajin Sabubu. Wani jami’in soji na sashin fasaha ya shaidawa PRNigeria cewa bayan samun bayanin taruwar su, nan take sojin sama suka kaddamar da…

Read More

Neja: Luguden Bama-Bamai Ya Hallaka ‘Yan Bindiga 70

Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar ayyukan hadakar sojojin sama dana kasa na Operation Gama Aiki (OPGA) suna kara samar da nasarori na ban mamaki a cigaba da farautar ‘yan Bindiga da suke yi a fadin jihar. An tattaro bayanai akan yadda ‘yan bindigan dake da sansani a yankin Jasuwan Garba-Urege a jihar Neja sun sha ragargaza a wurin sojojin sama na OPGA da suka yi amfani da Agusta 109 da EC 135 jiragen yaki. Yadda ragargazar ta kasance Wani babban jami’in tsaro wanda har da shi aka yi…

Read More

Borno: Dakarun Soji Sun Yi Wa Mayakan Boko Haram Kisan Kiyashi

Rahotanni daga Jihar Borno na bayyana cewar Rundunar sojin ?asa tace sojoji sun dakile yunkurin yan ta’adda na kai hari garin Damboa a jihar Borno ranar Lahadi, inda suka yi nasarar karkashe da dama daga cikin su. An ruwaito cewa gwarazan sojin sun ci karfin yan ta’addan bayan dogon musayar wuta, wanda hakan yasa suka tsere bayan kashe da dama daga cikin su. Kakakin rundunar soji ta ?asa, Onyema Nwachukwu, a wani jawabi da ya fitar yace maharan sun kone motocin jami’an sa kai JTF guda biyu yayin fafatawar. Ya…

Read More

Neja: ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Kwamishina Sun Bukaci Miliyan 500

Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar ‘Yan bindigar da suka tsare kwamishinan harkokin yada labarai na jihar, sun tuntubi ‘yanuwansa, sun bukaci a biya kudin fansa na miliyoyin kudade. An ruwaito cewa ‘yan bindigan da su ka yi garkuwa da Malam Sani Mohammed Idris, sun fada wa iyalinsa su kawo Naira miliyan 500. Rahoton da aka fitar a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021, ya ce miyagun ‘yan bindigan sun ce sai an biya kudin sannan kwamishinan zai fito. An yi garkuwa da Sani Mohammed Idris a jiya…

Read More