Miyyeti Allah Ta Yi Kiran Gaggawar Kama Wadanda Suka Yi Kisan Jos

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu ‘yan ta’adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, a ranar Asabar inda suka karkashe Mutane kimanin 30.

?ungiyar ta Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos ya fitar, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.

“Harin na kwanton baunar da ya faru da misalin karfe 10:00 na safe, ya kuma raunata matafiya da dama, yayin da wasu 40 kuma ba a ji duriyarsu ba.

“Matafiyan suna cikin ayarin motocin bas guda hudu, lokacin da aka kai musu hari. “Miyetti Allah ta yi Allah wadai da wannan tashin hankali mara ma’ana akan matafiya. “Muna kira ga hukumomin tsaro da su zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aikin kuma su gurfanar da su a gaban kuliya.”

Related posts

Leave a Comment