Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar ayyukan hadakar sojojin sama dana kasa na Operation Gama Aiki (OPGA) suna kara samar da nasarori na ban mamaki a cigaba da farautar ‘yan Bindiga da suke yi a fadin jihar.
An tattaro bayanai akan yadda ‘yan bindigan dake da sansani a yankin Jasuwan Garba-Urege a jihar Neja sun sha ragargaza a wurin sojojin sama na OPGA da suka yi amfani da Agusta 109 da EC 135 jiragen yaki.
Yadda ragargazar ta kasance Wani babban jami’in tsaro wanda har da shi aka yi ragargazar ya ce sai da jirgin saman ya bi a sannu wurin gano asalin wuraren da miyagun mutanen suka yi dandazo sannan ya harba abubuwa masu fashewa a wuraren.
An hango yadda sansanonin nasu suka yi ta kamawa da wuta sakamakon harbin da suka sha. Rahotonni daga mazauna yankin sun tabbatar da yadda ‘yan bindiga 70 suka bakunci lahira.
Anyi wannan ragargazar ne a ranar 5 ga watan Augustan 2021. Kuma makamancin haka ya kara aukuwa a ranar 6 ga watan Augustan 2021 wanda sojojin sama suka yi a Kwawu da Uzawo dake jihar Neja inda aka ragargaji ‘yan ta’adda da dama.
