

Rudunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da mutane sha hudu wadanda ake zargi masu yin garkuwa da mutane ne a wurare daban daban dake fadin jahar.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yola.


D S P Suleiman Nguroje yace an kama mutanen ne a maboyarsu dake wurare daban daban karkashi jagorancin Jami an tsaro na SIB dake jahar ta Adamawa.
Sanarwa taci gaba da cewa mutanen da ake zargin sun amsa cewa sune sukayi garkuwa da Alh. Sale Idi dake zaune a kauyen Faran dake cikin karamar hukumar Fufore,sai Alh. Ya u Adamu dake cikin karamar hukumar Ganye tare kuma da Jones Hayatu wanda ke kauyen Kojoli a karamar hukumar Jada dukkanninsu a jahar Adamawa kuma saida suka karbi makuden kudin fansa kafin suka sakosu,
Kwamishinan yan sandan jahar ta Adamawa CP Aliyu Adamu ya yabawa Jami an tsaron SIB bisa wannan namijin kokari da sukayi wajen kama mutanen. Don haka nema kwamishinan ya kirayi al umma da sukasance masu taimakawa hukumomin tsaro da wasu bayanai da zai basu damar kama masu aikata laifi a tsakanin al umma.
Kwamishinan ya kuma bada umurni da a gudanar da bincike domin gabatar da wadanda ake zargin gabab kotu domin su fuskanci shariya.
