Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su tabbata sun kamo duk wa?anda ke da hannu a kasar matafiya da matsasa ?auke da makamai suka yi Jos, Jihar Filato.
Kakakin fadar shugaban kasa, Garba shehu ya fitar da wannan sanarwa da ya ke kunshe da sakon shugaban kasa.
Sanarwar ta cigaba da cewa shugaba Buhari ya ce gwamnati ba za ta sa ka ido kawai wasu gungun b?ata gari su riki yin abinda suka dama kuma a kyale su ba.
” Wannan hari ba rikin Makiyaya da Manoma bane, wasu ne kawai suka bushi iska suka aikata hakan.
Shehu ya ce an gano cewa karara maharan sai da shirya tsaf kafin suka aikata abinda suka yi. Suka kashe wadanda zasu kashe sannan sukka jibwa wasu rauni.
Buhari ya yaba wa ?okarin da gwamnatocin jihohin Ondo, Bauchi, Filato, Sheikh ?ahiru Bauchi da sarkin musulmi suke yi domin tausa mutane kada abin ya fi haka
Jami’an tsaro a jihar Filato sun bayyana cewa sun kama matasa 6 cikin gungun matasan da suka tare motocin wasu matafiya da suka fito jihar Bauchi taron zikiri.
Mun kawo muku labarin yadda wasu matasa ?auke da makamai suka afka wa motocin matafiya da suka fito taron Zikiri a garin Bauchi ranar Asabar suka kashe mutane har sama da 20.
Wa?annan mutane da aka kadhe suna hanyar su ta komawa jihar Ondo ne bayan halartar taron zikiri wanda sheikh Dahiru Bauchi yayi gayyata akai.
Matasan ?auke da muggan makamai sun tare wasu manyan motocin bas mai cin mutum 18 a hanyar Jos zuwa Zaria inda suka far musu suka kashe akalla mutum sama da 20.
Matafiyan na dawowa daga taron zikirin murnar shiga sabuwar shekarar musulunci wanda aka yi a garin Bauchi bisa gayyatar Sheikh Dahiru Bauchi.
Majiya ta bayyana cewa koda motocin suka isa gada-biyu dake karamar hukumar Jos ta Arewa sai matasan suka dira musu, suka fara sara suna duka.
” Mutum sama da 80 sun arce cikin daji. Sannan kuma na ga wasu gawarwaki har 22 wa?anda na ?irga da kai na a asibitin koyarwa na jami’ar Jos.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya umarci rundunar ?an sandan jihar su bi sako-sako duk inda za shiga su tabbata sun kama wa?anan matasa da su aikata wannan mummunar abu.
