Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya bu?aci mazauna garuruwan da ‘yan bindiga ke yawan kai wa hare-hare da su nemi makamai don kare kan su daga hare-haren.
Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da ya kai ziyarar jaje a ?aramar Hukumar Jibia ga iyalan mutum 10 da jami’an hukumar kwastan suka kashe a makon da ya gabata.
Katsina na cikin jihohin da ‘yan bindiga suka fi kashewa tare da yin garkuwa da mutane a arewa maso yamnmacin Najeriya.
Ranar 11 ga watan Disamba ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka sace ?alibai daga sakandaren garin Kankara na jihar ta Katsina guda 344, inda suka shafe kwana shida a hannun masu garkuwar.
“Mi?a wuya da mutane ke yi ga ‘yan fashi shi ke jawo ?arayin su ci gaba da aikata munanan lamura a lokuta da yawa,” a cewar Masari cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Abdu Labaran Malumfashi ya fitar.
Ya ?ara da cewa “wajibi ne mutane su daina tunanin cewa harkar tsaro ta gwamnati ce ita ka?ai”.
Kazalika, gwamnan ya umarci mutanen yankin da kar su yarda da duk wani ihsani da hukumar kwastan za ta yi musu “har sai an nema wa iyalan wa?anda aka kashe ha??insu”.
