Yan bindigan da suka sace malamai da ?alibai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura, jihar Zamfara, sun nemi a basu miliyan N350m ku?in fansa.
Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntu?e shi ta wayar salula.
Yace yan bindiga sun nemi a ba su miliyan N350m ku?in fansar mutum 20 dake hannun su a yanzun sannan su sako su.
Mainasara yace:
“Sun fa?a mun cewa sai an basu kudin da suka bukata kafin su sako ?alibai da malaman da suka kwashe a makarantar da nake jagoranta.”
Wa zai biya wa?annan makudan ku?i?
Sai dai shugaban makarantar bai fayyace cewa iyalan wa?anda aka sace ne zasu biya wa?annan ku?a?en ko kuwa gwamnatin jihar Zamfara.
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Muhammad Shehu, yace sam hukumar yan sanda bata san ?arayin sun nemi kudin fansa ba.
Shehu yace:
“Bamu da masaniya game da bukatar yan bindigan na ku?in fansa amma muna iyakar bakin kokarin mu wajen kubutar da gaba ?aya wa?anda aka sace.”
