Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro a fadarsa a ranar Alhamis kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce Buhari wanda ya dawo daga London a ranar Juma’a zai gana da shugabannin tsaron ne domin tsara tsare-tsaren kawo ?arshen ?alubalen tsaro da ke gabansu.
Sanarwar ta ce jami’an tsaron ?asar sun ?ara ?aimi wajen ya?i da masu tayar da ?ayar baya da ?an fashin daji da sauran masu aikata laifuka da suka addabi ?asar wa?anda hakan ke sa suke mi?a wuya.
Ganawar ta ranar Alhamis a cewar sanarwar, ta shafi sanar da shugaban ?asa kan ci gaban da aka samu a yakin da ake yi gadan gadan da masu tada kayar baya a fadin kasar.
