Kungiyar tuntuba ta Dattawan Arewa Arewa Consultative Forum, ta yi watsi da maganar yafewa yan ta’addan Boko Haram da suke mika wuya ga gwamnati da kuma sakinsu, kamar yadda gwamnati ta kuduri aniyar yi.
Shugaban kungiyar na kasa, Cif Audu Ogbeh, ya ce wajibi ne a hukunta yan ta’addan kan laifukan da suka aikata kan yan Najeriya, cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.
Ogbeh, wanda tsohon Ministan noma ne, ya bayyana hakan a jawabin da ya rattafa hannu kuma kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe, ya sake a Kaduna ranar Talata.
“Muna ganin yadda yan ta’addan Boko Haram ke mika wuya da yawansu. cikinsu akwai masu hada bama-bamai, kwamandoji, masu fyade, da masu satan yara.” “Saboda haka me zamuyi da su? Kawai mu sake su kuma mu yarda da su? Gaskiya da kamar wuya.”
Kungiyar tace idan har za’a saki wadannan mutane to a saki dukkan mutanen da aka tsare a gudan yari a fadin Najeriya gaba daya.
“Muna taya gwamnan Borno, Shehun Borno, Sanata Ndume, da daukacin yan Najeriya wajen nazari kan wannan lamari kuma shawararmu itace: A hukuntasu ko kuma a saki dukkan wadanda ke tsare a fadin tarayya.”
