Zan Murkushe Duk Wani Dan Ta’adda A Zamfara- Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin Gusau na bayyana cewar Sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, Yakubu Elkana, ya ja kunnen shu’uman ‘yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara inda yace ko dai su zubar da makamansu ko kuma su fuskanci hukunci mai muni.

Kwamishina Elkana ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Laraba, inda ya hori ‘yan bindiga suyi gaggawar baiwa gwamnatin jihar hadin kai wurin samar da zaman lafiya ko kuma su ga aiki da cikawa.

Tsarin aikina cikin dabara zai fara, zamu yi amfani da salo na musamman wurin bi daki-daki don kawo karshen rashin tsaro a fadin jihar nan.

Zamu zabura wurin mayar da hankali akan yaki da duk wasu ‘yan ta’adda da masu taimaka musu su fuskanci hukunci daidai da laifinsu ta hanyar amfani da jama’an gari wurin cimma wannan kudiri namu.

Jajircewarmu da mayar da hankalinmu a matsayin jami’an ‘yan sanda zai taimaka mana wurin gaggawar kawo karshen ta’addanci a jihar nan, sannan zamu yi amfani da tsare-tsaren da sifeta janar na ‘yan sanda ya samar da kuma hanyar samar da zaman lafiya da gwamna Bello Matawalle ya kirkiro.

Wannan shine abinda na mayar da duk hankalina akai a matsayina na kwamishinan ‘yan sandar jiharnan,” a cewar Elkana.

Sannan kwamishinan ya kara da rokon jama’an gari da su yi kokarin baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai wurin dakatar da duk wasu ta’addanci a fadin jihar. A karkashin mulkina, ‘yan sanda zasu yi kokarin ganin sun yi amfani da kwarewa irin tamu don shawo kan kowacce irin matsala.

Zamu bi wasu hanyoyin don dakatar da ta’addanci, shiga hakkin bil’adama, rashawa da sauran miyagun ayyuka a fadin jiharnan,” a cewarsa.

Related posts

Leave a Comment