Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa an sace ?alibai da dama da malamai a Kwalejin Noma da ke garin Bakura.
Mataimakin rijistara na kwalejin Malam Aliyu Bakura, ya tabbatar wa da BBC wannan labari.
Ya ce ‘yan Bindigar sun kashe mutum hu?u da suka ha?a da ?an sanda ?aya da masu gadi uku.
Ya ce “a jiya Lahadi da daddare wajen ?arfe 10 suka shiga suka yi ta harbe-harbe suka kwashe ?alibai 15 da kuma wani malami da matarsa da ?a?ansa biyu,” a cewarsa.
Malam Aliyu ya ce maharan suna da matu?ar yawa kuma sun haura katanga ne sannan sun fi awa biyu a cikin makarantar suna harbe-harbe.
Shekara biyu da suka gabata ma mahara sun taba shiga kwalejin suka sace matar shugaban makarantar.
