Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana adadin wasu mutane masu yawa sun rasa ransu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Gora Gida, karamar hukumar Zangon Kataf, dake kudancin jihar Kaduna a karshen mako.
Da yake magana da manema labarai Hakimin Gora, Mr Elias Gora, yace yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi. Ya kara da cewa wata mata ta samu raunin harbin bindiga sannan kuma maharan sun kona mota guda ?aya.
Mr. Gora ya kara da cewa mutum biyu daga cikin wa?anda aka kashe sun kasance mahaifi ne da ?ansa, kuma nan take suka mutu sakamakon harbin Bindiga.
“Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi, inda suka kashe mahaifi da ?ansa da kuma wani mutum ?aya.” “Yan bindiga sun harbi wata mata ?aya sannan kuma sun kona mota guda ?aya a yayin harin.”
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya ?i daga kiran wayar da ake masa don jin ta bakinsa. Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton hukumar yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa game da harin ba a hukumance ba.
