Kisan Jos: Mun Zuba Ido Muga Matakin Da Gwamnati Za Ta Dauka – Jingir

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Shiekh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga Musulmi a fadin kasar nan da su kwantar da hankalinsu bayan kisan matafiya musulmai da aka yi a Jos ranar Asabar.

Ya yi wannan kira ne a wata hira da manema labarai ranar Lahadi a Jos, dangane da kisan gilla da wasu Matasan Kiristoci suka yi wa Musulmi matafiya har su 33 a garin Jos.

Ya ce duk da kisan yana da zafi da bakin ciki, amma bai kamata mutane su dauki doka a hannun su ba. Sai dai malamin ya bukaci a gaggauta kamawa tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Sheikh Jingir ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su tabbatar da adalci ga matafiyan da basu ji ba basu gani ba.

“Wannan ba shi ne karon farko da aka kama matafiya Musulmi aka kashe su a kan manyan hanyoyi ba. “Me ya sa mutane za su ci gaba da aikata irin wannan danyen aikin kuma su tafi salin-alin? ba daidai bane.

Sheikh Jingir, ya ce a duk lokacin da gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai binciki wata matsala, da kyar za a yi wani abu game da sakamakon kwamitin, tare da fatan wadanda suka aikata wannan aikin ba za su tsira ba.

Related posts

Leave a Comment