Rahotanni daga Jihar Borno na bayyana cewar Rundunar sojin ?asa tace sojoji sun dakile yunkurin yan ta’adda na kai hari garin Damboa a jihar Borno ranar Lahadi, inda suka yi nasarar karkashe da dama daga cikin su.
An ruwaito cewa gwarazan sojin sun ci karfin yan ta’addan bayan dogon musayar wuta, wanda hakan yasa suka tsere bayan kashe da dama daga cikin su.
Kakakin rundunar soji ta ?asa, Onyema Nwachukwu, a wani jawabi da ya fitar yace maharan sun kone motocin jami’an sa kai JTF guda biyu yayin fafatawar. Ya kara da cewa a halin yanzun sojoji sun bazama nemo yan ta’addan wa?anda suka tsere.
Wani sashin jawabin yace: “Dakarun sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wani yunkurin kai hari garin Damboa da safiyar Lahadi, wanda mayakan Boko Haram/ISWAP suka so kaiwa.”
