Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sako Daliban Islamiyyar Tegina

Rahotanni dake shigo mana yanzu daga Jihar Neja na bayyana cewa an saki sama da ?aliban Islamiyyar Tegina 80 da ?an bindiga suka sace a jihar Neja. Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar mata da cewa suna hanyar Minna ta Kagara bayan ?antosu daga dajin Birnin Gwari. ?aliban sun shafe kwanaki 88 a hannun ?an bindiga da suka yi garkuwa da su.Article share tools A wasu rahotanni da muka kawo muku a baya sun bayyana 6 daga cikin daliban sun rigamu gidan gaskiya a hannun ‘yan Bindigan.

Read More

Matsalar Tsaro: Lokaci Ya Yi Na Sanya Dokar Ta Baci A Arewa – Matawalle

Mai girma gwamnan Jihar zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa lallai yanzu lokacin sa dokar ta Baci a fannin tsaro musamman a jihohin arewa. Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne yayin ganawa da mataimakin insfecta janar na Yan sanda na kasa Ali Janga a fadar gwannatin jihar zamfara yayin ganawar su a yau laraba. Matawalle yace kusan kowace jiha a arewa na fama da nata salon ayyukan ta’addanci Wanda Kullum hakan na janyo koma baya ga yankin mu. Ya Zama dole a Dau mataki tun yanzu kamin lamarin ya durkusar…

Read More

Masu Hankoron A Raba Najeriya Na Cikin Rudu – Sanusi

Tsohon Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi na biyu ya bayyana cewa masu Kiran a raba Najeriya suna aikata babban kuskure, kuma tabbas suna cikin rudu. Khalifan ya bayyana hakan ne lokacin wani biki a Lagos wanda aka shirya domin taya shi murnar cika shekara 60 da haihuwa, Khalifa Sanusi ya ce akwai bukatar kasar ta kasance a dunkule sannan a gudanar da mulki cikin adalci a kasar. A cikin jawabin nasa tsohon Sarkin na Kano ya kuma nuna takaicin yadda wasu shugabanni a Najeriya ba sa mayar da hankali wajen…

Read More

Harin NDA: Babu Gaskiya A Labarin Barci Ya Kwashe Sojoji – Rundunar Soji

Rahotanni daga Hedkwatar tsaro ta ?asa na bayyana cewar Rundunar sojin Najeriya ta ?aryata wasu rahotannin da suka ce sojojin da ke bakin aikin tsaron Kwalejin Horon Sojoji ta NDA bacci suke lokacin da ?an bindiga suka kai hari wanda ya kai ga kashe sojoji biyu da sace soja ?aya. Sanarwar da babban jami’in ya?a labarai na rundunar sojin ya fitar Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr ya ce labarin da wasu jaridu suka wallafa ba gaskiya ba ne inda ya ?alubalanci jaridun su bayar da shaidar da ke tabbatar da…

Read More

Ku Kare Kanku Daga ‘Yan Bindiga – Kiran Minista Ga ‘Yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta baiwa ?an Najeriya shawarar su tashi tsaye dan kare kansu daga hare-haren ?an Bindiga dake kaiwa. Ministan harkokin ?an sanda, Muhammad Dingyadi ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai. Yana amsa tambaya ne kan umarnin da gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya baiwa jama’ar jiharsa kan su mallaki makamai dan kare kansu. Dingyadi ya bayyana cewa kowa na da ra’ayinsa kuma watakila gwamnan ya ga cewa, hakan ne zai kawowa jiharsa maslaha. Yace amma abinda suke cewa, shine kada mutum ya mallaki makami ta…

Read More

Matsalar Tsaro: Lokaci Ya Yi Na Sanya Dokar Ta Baci A Arewa – Matawalle

Mai girma gwamnan Jihar zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa lallai yanzu lokacin sa dokar ta Baci a fannin tsaro musamman a jihohin arewa. Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne yayin ganawa da mataimakin insfecta janar na Yan sanda na kasa Ali Janga a fadar gwannatin jihar zamfara yayin ganawar su a yau laraba. Matawalle yace kusan kowace jiha a arewa na fama da nata salon ayyukan ta’addanci Wanda Kullum hakan na janyo koma baya ga yankin mu. Ya Zama dole a Dau mataki tun yanzu kamin lamarin ya durkusar…

Read More

Harin Makarantar NDA: Dattawan Arewa Sun Yi Kiran A Kori Mungono

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kungiyar dattawan arewa ta koka a kan tabarbarewar rashin tsaro sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai barikin Afaka dake NDA. An ruwaito cewa Shugaban kungiyar CNEPD, Zana Goni ya bayyana hakan ne a wata takarda da kungiyar ta fitar ranar Laraba inda yace duk matsayin mutum da kuma inda yake zama ba zai tsira daga ta’addanci ba kenan a kasar nan, tabbas abubuwa sun lalace. Kungiyar ta bukaci a tsige Monguno Sakamakon haka ne ya bukaci a tube mai bayar da shawara…

Read More

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Bukaci Fansar Miliyan 200 Na Sojan Da Suka Sace

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Yan bindigan da suka kai hari makarantar horar da Sojojin Najeriya NDA dake garin Afaka a jihar Kaduna kuma sukayi awon gaba da jami’in Soja sun kira gidan Soja inda suka bukaci ku?in fansa. Sojan da akayi awon gaba da shi sunansa, Manjo Dantong. A cewar FIJ, yan bindigan sun kira NDA domin tattauna maganar kudin fansa kafin su sake shi. Sun bukaci a basu kudi N200m idan har ana son Manjon ya dawo da ransa. Wata majiyar FIJ ta bayyana cewa: “Ko…

Read More

Sau 50 Boko Haram Na Yunkurin Hallaka Ni – Gwamna Zulum

Rahotanni daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum ya shaida cewa sau 50 yana tsallake rijiya da baya daga hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai masa. Gwamnan ya shaida hakan ne a lokacin wata tattaunawa da ?an jarida a fadar gwamnatin Abuja bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari. Jaridar Daily Trust ta rawaito gwamnan na cewa sama da ?an Borno dubu 100 aka kashe a rikicin Boko Haram na tsawon shekara 12. Sannan ya kuma shaida cewa akwai maya?a 2,600 da suka mi?a…

Read More

Harin NDA: Rundunar Soji Ta Yi Rantsuwar Daukar Fansa

Hedikwatar tsaro a Najeriya ta lashi takobin lalubo ?an bindigar da suka kashe tare da sace wasu jami’an sojoji bayan wani hari da suka kaddamar a makantar soji ta NDA a Kaduna. Wasu mazauna gidajen da ke NDA sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace guda ?aya yayin harin da suka kai ranar Litinin da tsakar dare. Sanarwar da shugaban hafsoshin sojin Najeriya Janar Lucky Irabor ya fitar, ta mika sakon ta’azziya ga iyalan sojojin da aka kashe, sannan ya shaida cewa…

Read More

Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kwalejin Soji Ta NDA Dake Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta Nigeria Defence Academy, NDA, da ke birnin Kaduna. Wasu mazauna gidajen da ke NDA sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace guda daya yayin harin da suka kai ranar Litinin da tsakar dare. Sanarwar da mai magana da yawun Makarantar Sojojin Bashir Muhammad Jajira ya fitar daga bisani ta tabbatar da kai harin. Ya ce ‘yan bindigar sun shiga bangaren gidaje na Makarantar inda suka…

Read More

Adamawa: An Damke Daliban Da Suka Kashe Wata Budurwa

Rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama wasu dalibai da kisan wata budurwa mai suna Franca Iliya wanda kuma dukkanisu dalubenai a kwaljin fasaha ta tarayya dake Mubi a jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar ta Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya tabbatarwa muryar yanci haka a ofiahinsa dake ahelkwatan rundunan dake yola. D S P Suleiman Nguroje yace an samu nasaran kama wadanda ake zarginne biyo bayaran rahoton da auka samu wanda hakan yasa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Aliyu Adamu baiyi da…

Read More

Ina Nan Akan Bakana Na Kowa Ya Nemi Makami Don Kare Kai – Masari

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamna jihar Aminu Bello Masari ya yi watsi da kiran kungiyar arewa (CNG) na yayi murabus saboda yace mutane su kare kansu daga yan bindiga. Masari yace ba shine gwamnan farko da ya fa?awa mutane su kare kansu daga ta’addancin yan bindiga ba, kuma ya fadi hakan ne saboda shine mataki na karshe. Gwamnan ya kara da cewa kiran da ake masa ya yi murabus daga kujerarsa wata alama ce ta rashin fahimtar halin da kasar nan take ciki gaba ?aya. Jihar Katsina…

Read More

Adamawa: An Yi Nasarar Damke Gogaggen Dilar Wiwi

Rundunan ‘yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran mutumin da ake zargi dilar tabar wiwi ne, wanda ke gudanar da harkokinsa acikin kananan hukumomin Ganye, Jada, da kuma karamar hukumar Mayo Belwa dake jahar Adamawa. Kakakin rundunŕn yan sandan a jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar akarabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Wanda ake zargin mai suna Zingina maigari dan shekaru ashirin da shida da haihuwa Wanda ke zaune a anguwar barde a cikin karamar hukumar…

Read More

Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sako Wasu Daliban Bethel Baptist Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Yan Bindigar da suka sace daliban Makarantar Bethel Baptist sun saki ?alibai 15 daga cikin wa?anda suka sace a sakandaren ta Jihar Kaduna. Shugaban ?ungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ya shaida wa BBC Hausa cewa an saki ?aliban ne da daren Asabar bayan an biya ku?in fansa. Ya ce har yanzu akwai yara 65 a hannun ‘yan bindigar, yayin kusan 53 suka ku?uta. A ranar 25 ga Yuli aka saki 28 daga cikinsu. ‘Yan bindigar sun sace yaran…

Read More

Sama Da Mutum Dubu 50 Sun Yi Hijira Daga Sokoto Zuwa Nijar

Sama da mutane 50,000 a garuruwa 17 dake karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa jamhuriyyar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga.Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltan mazabar Sabon Birni ta Arewa, Aminu AlMustapha Boza, ya bayyana hakan, rahoton DailyTrust. Boza yace yanzu haka mutan wadannan kauyuka suna neman mafaka a kauyen Tudun Sunnah, dake karamar hukumar Gidan Runji, jihar Maradi a jamhuriyyar Nijar. Dan majalisan ya kara da cewa ya dade yana kokarin ganin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kan lamarin amma abin ya…

Read More

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Arce Da Mutum 60 Dokar Daji

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun yi garkuwa da gwamman mutane bayan wani hari da suka kai a ?auyen Rimi da ke ?aramar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara ranar Juma’a. Kwamishinan Ya?a Labarai Ibrahim Dosara ya tabbatar da kai harin, yana mai cewa kusan mutum 60 ne ‘yan bindigar suka sace, amma ya ce ba a tabbatar da adadin ba tukunna. “A safiyar yau [Juma’a] mun tashi da labarin cewa ‘yan fashi sun afka wa ?auyen Rimi sun sace mutum 60, duk da cewa ba a…

Read More

Filato: An Rufe Jami’ar Jos Saboda Matsalar Tsaro

Hukumar Jami’ar Jos ta dakatar da ayyukan karatu tare da rufe ta baki ?aya saboda kisan ?alibai da ke ?aruwa a kusa da makarantar” jim ka?an bayan sassauta dokar hana fita da aka saka. A cewar wata sanarwa da Rajistira Monday Danjem ya sanya wa hannu, an umarci dukkan ?alibai da su koma gida ko kuma wani wuri mai kwanciyar hankali har sai hankula sun kwanta. Kazalika, hukumar makarantar ta dakatar da jarrabawar da ta shirya farawa ta shekarar karatu ta 2019/2020. Matakin jami’ar ya biyo bayan kisan wasu matafiya…

Read More

Kaduna: ‘Yan Bindiga Da Dama Sun Mutu A Rikicin Cikin Gida

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Hukumomi a jihar sun ce wasu mambobin kungiyoyin ‘yan bindiga da ke gaba da juna su tara sun rasa rayukansu sanadin musayar wuta a yankin ?aramar hukumar Giwa. Gwamnatin jihar Kaduna ta ce rikicin ya faru ne a wani ?auye da ke ?aramar hukumar ta Giwa. Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya ce majiyoyin tsaro sun ba da rahoton cewa wani shahararren dan fashi da aka fi sani da ‘Godon Mota’ da yaransa sun abka wa kauyen Garke a ranar…

Read More

Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda Ta Kafa Sabon Kwamitin Bincikar Kyari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kafa wani sabon kwamiti na cikin gida wanda zai yi bincike mai zurfi a kan Takardun da FBI ta Amurka ta gabatar wadanda suka janyo dakatar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari. Ana zargin Abba Kyari, wanda shine tsohon shugaban IRT da amsar rashawa daga hannun wani rikakken dan damfarar yanar gizo, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi. An ruwaito yadda Kwamitin bincike na ‘yan sanda wanda sifeta janar na ‘yan sanda,…

Read More