Zamfara: Farmakin Soji Ya Bar Tulin Gawawwakin ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar wani harin ha?in guiwa da sojojin sama da na kasa suka kai dajin Sabubu dake jihar Zamfara karkashin Operation Hadarin Daji ya sa an hallaka yan bindiga da dama.

An ruwaito cewa an gano manyan yan ta’adda na ciki da wajen jihar sun taru a wani wuri da ake zargin ma?oyar kasurgumin ?an bindiga, Halilu Tubali ne a arewacin dajin Sabubu.

Wani jami’in soji na sashin fasaha ya shaidawa PRNigeria cewa bayan samun bayanin taruwar su, nan take sojin sama suka kaddamar da kai hari dajin, inda suka karkashe da dama daga cikin su.

Jami’in ya bayyana cewa an sanar da sojojin ?asa dake kusa da dajin su kasance cikin shiri domin kai hari dajin da zaran an gama ruwan bama-bamai ta sama. Jami’in yace: “Ranar 6 ga watan Agusta, mun samu bayanin sirri cewa anga isar manya-manyan yan bindiga dajin daga cikinsu har da Halilu Tubali, ?aya daga cikin manyan wa?anda ake nema.”

“Cikin hanzari aka tura jirgin yakin Alpha zuwa wurin, da zuwansa ya hangi yan ta’addan sun yi shigar bakaken kaya. Nan take ya fara sakar musu bam a karon farko inda ya kashe su da yawa.”

“Ragowar suka fara neman wurin ?uya, amma jirgin ya sake sako bam karo na biyu a dai-dai inda ya fahimci suna ?uya kuma nan take ya hallaka su.” Sojojin ?asa sun isa wurin bayan harin sama Rahoto ya nuna cewa ragowar da suka yi kokarin guduwa da manyan raunuka sun ha?u da sojojin ?asa, inda suka karasa hallaka su.

Wannan harin yasa sojoji sun samu nasarar kashe fiye da yan bindiga 45 amma babu tabbas ko an kashe jagoransu Halilu Tubali. Amma ?aya daga cikin yan ta’addan da aka samu bai karssa mutuwa ba ya tabbatar da cewa harin sama ya yi kaca-kaca da mafi yawansu.

Related posts

Leave a Comment