Kungiyar Kiristoci Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Musulmi A Jos

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Filato, a ranar Lahadin da ta gabata ta yi Allah wadai da kisan wasu matafiya musulmai 25 a hanyar Rukuba, a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar.

Rev. Fr. Polycarp Lubo, shugaban CAN a jihar, ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka aikata danyen aikin, domin hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Wasu fusatattun matasa da ake zargin ‘yan ?abilar Irigwe ne suka kai hari kan motocin bas guda biyar dauke da matafiya Musulmai sama da 90, suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Mista Lubo ya kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da ke faruwa a kananan hukumomin Bassa, Riyom, Jos ta Kudu da Barkin Ladi duka dake Jihar Filato dake yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya.

A cewarsa: “Shugabancin CAN gaba daya ya la’anci wadannan hare-hare tare da rokon jami’an tsaro da su tabbatar da an dawo da zaman lafiya.

CAN ta tura sakon jaje ga iyalan wadanda aka cutar ”Muna jajantawa ga iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu, da kuma wadanda aka raba da muhallansu ko kuma aka yi musu lahani ko wane iri.

“Muna kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta cafke duk wadanda ke da hannu, don kawo karshen kashe-kashen da basu dace ba.” Mista Lubo ya ce kungiyar za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya a jiha.

Related posts

Leave a Comment