An bayyana cewar rashin daukar matakin hukunta masu aikata manyan laifuka na ta’addanci a Najeriya shine dalilin da ya sanya har yanzu ayyukan ta’addanci suka ki karewa a Najeriya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani Basarake a Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba Jakadan Hayin Banki a lokacin da yake tsokaci dangane da kisan matafiya sama da 30 da wasu tsagerun matasa suka yi a Jos babban birnin Jihar Filato.
Gambo Abba ya bada misali da abin da ya faru a shekarun baya na rikicin Zangon Kataf, inda wasu mutane saboda dalilan son zuciya suka kaddamar da kisa akan bayin Allah wadanda basu ji ba basu gani ba, amma abin mamaki daga bisani aka yi musu afuwa.
Abdullahi Gambo Abba ya kara da cewar tun daga wannan lokaci ya zamana sauran miyagu suka gane cewar idan sun aikata ta’asa babu wani abin da zai faru hakan ya sa abubuwa suka ci-gaba da dagulewa.
“Duk lokacin da aka wayi gari wadanda suka yi kisa suna cigaba da rayuwarsu hankali kwance, ‘ya’yan wa?anda aka kashe suna kallon su, tabbas da akwai gagarumar matsala”.
Daga ?arshe Jakadan Hayin Banki ya shawarci gwamnati da ?aukar matakan hukuncin da ya dace akan dukkanin wa?anda aka samu da laifi.
Sannan ya yi kira ga sauran jama’a da kar a ?auki doka a hannu abi doka da tsari.
