Rahotanni daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Gwamnatin Jihar Filato ta ce dokar hana fitar da ta saka ta zama ta zaman gida baki ?aya biyo bayan kashe matafiya Musulmai da “matasan ?abilar Irigwe” suka yi a Jos, babban birnin jihar.
Tun farko an ?a?aba dokar hana fitar ce daga 6:00 na yamma zuwa 60:00 na safe a ?ananan hukumomin Jos Ta Kudu da Jos ta Arewa da kuma Bassa. Amma ?arin ya shafi Jos ta Arewa ne ka?ai.
A ranar Asabar ne matasan suka tare matafiyan tare da kashe kusan mutum 30 sannan suka jikkata wasu kusan 50 a lokacin da suke wucewa ta cikin birnin zuwa Jihar Ondo bayan sun taso daga garin Bauchi.
Sanarwar ‘yan sanda ta ce mutum 25 aka kashe a harin tare da jikkata 33.
Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya ya tura tawagar bincike ta musamman ?ar?ashin jagorancin DIG Sanusi N. Lemu.
Ya ?ara da cewa rundunar ta kama mutum 20 da ake zargin aikata kisan sannan ta ceto mutum 33 da aka raunata yayin harin.
