Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Ayuba Dodo Dakolo, dagacin kauyen Rijana, ?aramar hukumar Kachia dake kudancin jihar a fadarsa. An ruwaito cewa sun sace Dagacin ne tare da wasu manoma a Kurmi, kusa da Chikwale dake yankin na Kachia. Kauyen Rijana na kan babbar hanyar Kaduna-Abuja da mutane ke yawan bi, kuma hanyar ta yi ?aurin suna saboda yawan harin yan bindiga, wa?anda ke tare matafiya su sace mutane. Wata majiya daga kauyen, ta shaida wa manema labarai ranar Alhamis…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Sai An Hada ?arfi Za A Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa a kasar da su ajiye batutuwan zabe a gefe guda kuma su hada hannu da gwamnatinsa a kokarin da take yi na magance matsalar tsaro a kasar. Shugaban ya bayyana haka ne yayin da wasu jami’an jam’iyun suke shan ruwa a Fadar Aso Rock tare da wasu manyan ‘yan kasuwar kasar, inda ya ce rashin tsaro shi ne babbar matsalar da ke damun kowane dan Najeriya. Shugaban ya ce a makon jiya, yayin taron babban kwamitin gudanarwa na jam’iyyarsa…
Read MoreAn Shiga Makoki Sakamakon Yawaitar Kashe-Kashe A Kudancin Kaduna
Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewar duba ga hauhawan matsalar rashin tsaro a jihar kungiyar shugabannin kirista a kudancin Kaduna sun kafa wani kwamitin mutum hudu don taron addu’a na wannan shekarar. Tsawon shekaru biyu kenan ba a gudanar da taron addu’an ba wanda aka saba yi duk shekara saboda annobar korona, da sauran kalubale na rashin tsaro. Da yake rantsar da kwamitin a ranar Laraba a garin Kafanchan, jim kadan bayan taron mika masa shugabanci, shugaban kungiyar, Dr. Emmanuel Kure, ya bukaci mambobin kwamitin da su jajirce wajen…
Read MoreNeja: Jirgin Yakin Soji Ya Hallaka Yara Bisa Kuskure
Rahotanni daga Minna babban birnin jihar Neja na bayyana cewar Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Matane, ya tabbatar da kashe kananan yara shida bisa kuskure wanda jirgin ya?in sojin sama ya yi a jihar. Sakataren gwamnatin na cewa sun gudanar da bincike don tabbatar da lamarin wanda ya faru a makon da ya shu?e. Ya ce kananan yaran sun rasa rayuwarsu ne yayin da jirgin ya?in ke aikin tarwatsa yan ta’adda a wasu sansanonin su dake cikin jihar. ” Lamarin ya afku bisa kuskure, gwamnatin Neja ta yi duba zuwa lamarin…
Read MoreDa Dumi-Dumi: Bam Ya Hallaka Sama Da Mutum 20 A Taraba
BASHIR ADAMU, JALINGO. Wasu da ba a san ko su waye bane sun tayar da nakiya a Mashayar Burkutu a Kauyen Iware, dake Karamar Hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba. Wani Shida daya gani da ido da baiso a anbaci sunansa ba yace, tashin nakiyar ya kashe a kalla mutane 20, tare da jikkata wasu mutane da dama, kana “tuni an garzaya da wadanda suka jikkata Karamin Asibitin Matakin Farko dake Iware, tare kai wasu Asibitin Kwararru da Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya dukkansu dake Jalingo. Ya kuma kara da cewa, tuni…
Read MoreDa Dumi-Dumi: Jirgin Saman Soji Ya Yi Hatsari A Kaduna
Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna yanzu na bayyana cewar wani Jirgin saman sojoji ya hatsari a Kaduna, yau Talata 19 ga Afirilu da misalin 7:39 Yamma. Majiyoyi sun ce ana fargabar mutuwar matukan jirgin biyu da ke cikinsa yayin hatsarin. Wata majiya ta shaida cewa, jirgin na Super Mushak na horar da jami’ai ya yi hatsari ne a cibiyar NAF ta Kaduna a lokacin da ya ke aikin horos da jami’an tsaron. Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Cdre Edward Gabkwet, bai amsa neman…
Read More‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Mummunan Hari A Jihar Neja
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar gungun wasu ‘yan Bindiga ?auke da muggan makamai yankunan Kadna da Naknuwape da ke Gwada a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja ruwan makamai. Majiyoyi sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun halaka dan sanda da wani mazaunin kauyen yayin da suka yi garkuwa da wasu mutum mutane. Jihar Neja na ?aya daga cikin Jihohin da ‘yan Bindiga ke addaba da yawan kashe kashe da garkuwa da mutane a ‘yan shekarun nan, lamarin da ya tilasta jama’a da dama yin…
Read MoreFilato: ‘Yan Bindiga Sun Yi Kisan Kiyashi
Rahotannin dake shigo mana daga Jos babban birnin jihar Filato na bayyana cewar hare-haren ‘yan Bindiga a yankin ya hallaka Sama da mutane 150 yayin damutum fiye da 4,000 ne aka raba da muhallansu. ‘Yan bindigar sun afka wa ?auyukan na ?aramar Hukumar Kanam a kan babura ranar Lahadi da ta gabata, inda suka kashe mutum a?alla 150 da kuma ?ona ?umbin gidaje, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC Hausa. ?an majalisar wakilai mai wakiltar maza?ar Pankshin/Kanam/Kanke, Yusuf Adamu Gagdi, ya fa?a wa BBC Hausa cewa akasarin ‘yan…
Read MoreZamfara: ‘Yan Bindiga Sun Sako Dalibai Mata Da Suka Sace
Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan Bindiga sun sako Dalibai Mata na Kwalejin Kimiyya Da Fasahar Lafiya Ta Tsafe Dake Jihar Zamfara Da Suka Sace Wata ‘yar uwar wadanda lamarin ya rutsa da su ta bayyana cewa iyayen yaran mata ne su suka hada kudi suka je daji da kansu suka karbo ‘ya’yansu. Sace sacen ?alibai musamman mata na ci wa jama’a tuwo a kwarya a Jihar Zamfara, inda ‘yan bindiga suka mayar da satar daliban a matsayin wata hanya ta cimma…
Read MoreZa Mu Samar Da Tsaro Ta Kowane Hali A Najeriya – Buhari
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da jerin hare-haren da aka kai wa?anda suka yi sanadin kashe sama da mutum 150 a jihar Filato. A martaninsa da ya bayar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce ba za a ta?a yafe wa “masu wannan aika-aika ba” kuma “ba za su samu rahama ba”. Ya dai bayyana lamarin a matsayin hare-haren ta’addanci. Shugaban kasar ya yi ta’aziyya ga iyalai da dangin mutanen da hare-haren suka shafa. ‘Yan bindiga ne a kan gomman…
Read MoreDa Dumi-Dumi: Za A Fallasa Wadanda Suka Shirya Harin Jirgin Abuja – Fadar Shugaban Kasa
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya tace nan bada jimawa ba, zata sanar da wa?anda suka ?auki nauyin kai harin Jirgin ?asan Abuja-Kaduna. Gwamnatin ta kuma bayyana mummunan lamarin aka abinda ya bayyana ha?in gwiwa tsakanin Boko Haram da ?an Bindiga dake gudanar da harin su a yankin.Ministan Tsaro Manjo-Janar Bashir Magashi Yace duk da Jami’an tsaro na yin bakin ?o?ari domin gano Dabar data kai harin, rahoto ta nuna cewa, ?ungiyar ?an bindigar tana ha?a hannu da wasu, yana mai kira ga…
Read MoreZamfara: An Shiga Firgici Sakamakon Sace Dalibai Mata Da ‘Yan Bindiga Suka Yi
Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun sace ?aliban Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya mata hu?u ranar Talata da dare. Wani mazaunin yankin ya fa?a wa BBC cewa maharan sun afka wa gidan da ?aliban ke zaune wanda ke wajen makarantar a garin Tsafe bayan sun tarar da jami’an tsaro na gadin kwalejin. Shugaban kwalejin, Yusuf Idris Maradun, ya ce ?alibai biyar ‘yan bindigar suka kama amma daga baya suka saki ?aya daga cikinsu saboda ta kasa tafiya sakamakon lalurar ?afa. Rundunar…
Read MoreBoko Haram Da ‘Yan Bindiga Sun Hade – Gwamnatin Tarayya
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin ta ce akwai ?awance tsakanin ?an bindiga masu satar mutane a yankin arewa maso yammaci da kuma maya?an Boko Haram. Ministan watsa labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa da shugaba Buhari ya jagoranta a fadarsa a Abuja. Ya ce abin da ke faruwa a yanzu akwai ?awance tsakanin ?an bindiga da Boko Haram, bayan an tambaye shi ya fa?i wa?anda suka kai hari a jihar Filato. Ya ?ara da cewa binciken farko kan harin jirgin ?asa…
Read MoreDa Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Dalibai Mata A Zamfara
Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun sace ?alibai mata hu?u a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya ranar Talata da dare a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya. Wani mazaunin yankin ya fa?a wa BBC cewa maharan sun afka wa gidan da ?aliban ke zaune wanda ke wajen makarantar a garin Tsafe bayan sun tarar da jami’an tsaro na gadin kwalejin. Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ce jami’an tsaro sun du?ufa domin ganin an ceto ?aliban da aka sace a gidan…
Read MoreYaki Da Ta’addanci Na Bukatar Taka Tsan-Tsan – Lai Mohammed
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa abu ne mai wahala a yaki yan fashin daji saboda yanayin da suke kai farmaki. Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a shirin gidan radiyo na Bond FM a karshen mako. Ya ce gwamnati mai ci ta zuba ku?i sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, inda ya kara da cewa kokarin zai fi yin tasiri ne idan al’umman kasar suka mara wa kokarin da gwamnati ke yi baya.…
Read MoreKaduna: ‘Yan Bindiga Na Cigaba Da Daukar Rayuka A Kauyuka
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar a ranar Lahadi ne al’ummar Kakura da ke karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna ta shiga tashin hankali, biyo bayan kisan da aka yi wa shugabansu Isiaku Madaki, lamarin da ya kai ga mutuwar wasu mutane 14 daban. An tattaro cewa an nada Madaki a matsayin shugaban al’ummar Kakura ne a ranar Asabar din jiya, kana a ranar Lahadi wasu ‘yan bindiga suka kashe shi. Lamarin ya haifar da wani hari da aka kai a wani matsugunin Fulani da ke yankin inda ake…
Read MoreFilato: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 26
‘Yan bindiga sun kashe mutum a?alla 26 cikin wasu hare-hare da suka kai a ?auyuka hu?u na Jihar Filato a ranar Lahadi. Maharan sun far wa ?auyukan ne da ke ?aramar Hukumar Kanam a kan babura, inda suka dinga harbe mutane tare da ?ona gidaje masu ?umbin yawa da kuma sace shanu. Mazauna yankin sun ce an ga gawar mutum 20 a garin Gyambau, sannan an ga wasu shida a Kyaram. Kazalika, an kai hare-hare a garuruwan Dungur da Kukawa. Mutane da dama ne suka ?ace kuma sakamakon harin.
Read MoreBorno: Sojoji Sun Yi Nasarar Kashe Babban Kwamandan ISWAP
Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Sojojin Najeriya sun kashe ?aya cikin manyan kwamandojin Iswap da wasu maya?a a wani farmaki a yankin arewa maso gabashi. Sojojin sun ce sun kashe kwamandan mai suna Abubakar Danbuduma da maya?a 19, yayin da suka kwato tarin makamai masu yawa. Rundunar sojin ta ce dakarunta sun kai harin ne a yankin Tafkin Chadi ta hanyar amfani da jiragen ya?i. Abu ne mai wahala a iya tantance gaskiyar labarin. Amma wannan na zuwa a yayin da maya?an Iswap ke kar?e…
Read MoreKisan Soji A Kaduna: Labarin Bai Cika Ba – Lai Mohammed
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Ya?a Labarai a Najeriya Lai Mohammed ya tabbatar da kai hari kan sansanin sojan ?asar da ‘yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna. Ministan ya ce duk da cewa kafofin ya?a labarai da dama sun ruwaito harin amma sun gaza wajen ruwaito yadda sojojin Najeriya suka fatattaki maharan. Sojoji a?alla 11 rahotanni suka ruwaito an kashe a harin na ranar Lahadi lokacin da maharan suka far wa sansanin nasu da ke yankin Birnin Gwari. Kazalika, an ?ona motocin soja masu sulke…
Read MoreMika Matatun Mai Ga Tompolo: Matasan Arewa Sun Gargadi NNPC
Kungiyar ha?in kan matasan Arewa ta yi tir gami da Allah wadai da yunkurin Kamfanin NNPC karkashin jagorancin Mele Kyari na mi?a kula da Matatun man fetur ga kasurgumin dan ta’adda Oweizide Ekpemupolo wanda aka fi sani da suna Tompolo. Matasan na Arewa sun yi wannan gargadi ne a wani taron manema labarai da suka kira wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna. Da ya ke jawabi a yayin taron mataimakin Kakakin ?ungiya na kasa Abdulsalam Mohammed Kazeem, yace kiran nasu ya zama wajibi duba da irin…
Read More