Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun sace ?alibai mata hu?u a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya ranar Talata da dare a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.
Wani mazaunin yankin ya fa?a wa BBC cewa maharan sun afka wa gidan da ?aliban ke zaune wanda ke wajen makarantar a garin Tsafe bayan sun tarar da jami’an tsaro na gadin kwalejin.
Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ce jami’an tsaro sun du?ufa domin ganin an ceto ?aliban da aka sace a gidan da suka kama haya suna kwana a cikin garin na Tsafe.
Shugaban Kwalejin Yusuf Idris Maradun ya ce ?alibai biyar ‘yan bindigar suka kama amma daga baya suka saki ?aya daga cikinsu saboda ta kasa tafiya sakamakon lalurar ?afa.
