Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Sako Dalibai Mata Da Suka Sace

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan Bindiga sun sako Dalibai Mata na Kwalejin Kimiyya Da Fasahar Lafiya Ta Tsafe Dake Jihar Zamfara Da Suka Sace

Wata ‘yar uwar wadanda lamarin ya rutsa da su ta bayyana cewa iyayen yaran mata ne su suka hada kudi suka je daji da kansu suka karbo ‘ya’yansu.

Sace sacen ?alibai musamman mata na ci wa jama’a tuwo a kwarya a Jihar Zamfara, inda ‘yan bindiga suka mayar da satar daliban a matsayin wata hanya ta cimma mummunar manufa.

Jihar Zamfara na sahun gaba a jihohin dake fama da matsalar tsaro a tarayyar Najeriya, ko a kwanakin baya mai girma Gwamna Muhammad Bello Matawallen ya samar da manyan motoci ga jami’an tsaro domin shawo kan matsalar.

Related posts

Leave a Comment