Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Ayuba Dodo Dakolo, dagacin kauyen Rijana, ?aramar hukumar Kachia dake kudancin jihar a fadarsa.
An ruwaito cewa sun sace Dagacin ne tare da wasu manoma a Kurmi, kusa da Chikwale dake yankin na Kachia.
Kauyen Rijana na kan babbar hanyar Kaduna-Abuja da mutane ke yawan bi, kuma hanyar ta yi ?aurin suna saboda yawan harin yan bindiga, wa?anda ke tare matafiya su sace mutane.
Wata majiya daga kauyen, ta shaida wa manema labarai ranar Alhamis cewa, yan bindigan sun tuntu?i shugabannin ?auyen, sun zayyana musu abu biyu da suke bukata.
Wasu daga cikin abubuwan da suka su?a bu?ata ya ha?a da Galan ?in Man Fetur, Ba?in man inji, da Sigari. Wani mazaunin ?auyen ya ce: “Mun yi magana da shugaban mu kuma yana cikin koshin lafiya, a yanzun sun nemi mu kai musu katin waya kuma sun yi barazanar kashe shi idan mu?a ki aiwatarwa.”
Yayin da aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai ?aga kiran wayar ba bare jin ta bakin hukumar su kan sace Dagacin. Amma wani babban jami’i ya shaida wa manema labarai cewa jami’an tsaro sun samu masaniya kan abun da ya faru.
