Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin ta ce akwai ?awance tsakanin ?an bindiga masu satar mutane a yankin arewa maso yammaci da kuma maya?an Boko Haram.
Ministan watsa labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa da shugaba Buhari ya jagoranta a fadarsa a Abuja.
Ya ce abin da ke faruwa a yanzu akwai ?awance tsakanin ?an bindiga da Boko Haram, bayan an tambaye shi ya fa?i wa?anda suka kai hari a jihar Filato.
Ya ?ara da cewa binciken farko kan harin jirgin ?asa da aka kai a Kaduna yna nuna “akwai ala?a tsakanin ?an bindiga da maya?an Boko Haram da ke yankin arewa maso gabashi.
