Za Mu Samar Da Tsaro Ta Kowane Hali A Najeriya – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da jerin hare-haren da aka kai wa?anda suka yi sanadin kashe sama da mutum 150 a jihar Filato.

A martaninsa da ya bayar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce ba za a ta?a yafe wa “masu wannan aika-aika ba” kuma “ba za su samu rahama ba”.

Ya dai bayyana lamarin a matsayin hare-haren ta’addanci.

Shugaban kasar ya yi ta’aziyya ga iyalai da dangin mutanen da hare-haren suka shafa.

‘Yan bindiga ne a kan gomman babura suka auka wa mutane da harbe-harbe tare da ?ona ?umbin gidaje a wasu ?auyuka a?alla hu?u cikin ?aramar hukumar Kanam ta jihar Filato, abin da ya tilastawa ?aruruwan mutane tserewa da gidajensu.

?auyukan da hare-haren suka shafa sun ha?ar da Gyambau da Kukawa da Kyaram da kuma Dungur.

Mafi yawan wa?anda aka kashe, an yi musu jana’izar bai ?aya a manyan kaburbura daidai lokacin da ake ci gaba da neman wasu ?arin gawawwaki a dazukan da ke kusa da ?auyukan.

Da yawan wa?anda hare-haren suka shafa, an kashe su ne lokacin da suka yi ?o?arin tserewa.

A kai ?umbin mutanen da suka jikkata zuwa asibitoci, akasarinsu da raunukan bindiga.

Lamarin na iya zama ?aya daga cikin hare-hare mafi muni da gungun ‘yan fashin daji suka kai tun bayan fara kashe-kashe da satar mutane don neman ku?in fansa sama da tsawon shekara goma a arewacin Najeriya.

Gwamnatin tarayya dai na shan gagarumar suka saboda gazawarta wajen shawo kan hare-haren da ke da?a ?azanta duk da tura dubban dakarun sojoji a sassan yankin.

Shugaba Buhari ya ba da umarni ga dakarun tsaro su gano wa?anda suka tafka aika-aikar kashe-kashen baya-bayan nan don gurfanar da su gaban hukunci cikin gaggawa, ya ?ara da cewa ko ta halin ?a?a sai an samu zaman lafiya a Najeriya.

Related posts

Leave a Comment