Da Dumi-Dumi: Jirgin Saman Soji Ya Yi Hatsari A Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna yanzu na bayyana cewar wani Jirgin saman sojoji ya hatsari a Kaduna, yau Talata 19 ga Afirilu da misalin 7:39 Yamma.

Majiyoyi sun ce ana fargabar mutuwar matukan jirgin biyu da ke cikinsa yayin hatsarin.

Wata majiya ta shaida cewa, jirgin na Super Mushak na horar da jami’ai ya yi hatsari ne a cibiyar NAF ta Kaduna a lokacin da ya ke aikin horos da jami’an tsaron.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Cdre Edward Gabkwet, bai amsa neman karin bayani daga majiya ba kan faruwar lamarin.

Related posts

Leave a Comment