Kaduna: ‘Yan Bindiga Na Cigaba Da Daukar Rayuka A Kauyuka

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar a ranar Lahadi ne al’ummar Kakura da ke karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna ta shiga tashin hankali, biyo bayan kisan da aka yi wa shugabansu Isiaku Madaki, lamarin da ya kai ga mutuwar wasu mutane 14 daban.

An tattaro cewa an nada Madaki a matsayin shugaban al’ummar Kakura ne a ranar Asabar din jiya, kana a ranar Lahadi wasu ‘yan bindiga suka kashe shi.

Lamarin ya haifar da wani hari da aka kai a wani matsugunin Fulani da ke yankin inda ake fargabar mutane 14 sun mutu.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi lokacin da Kiristoci ke shirin yin hidimar ibadarsu ta ranar Lahadi. Wani mazaunin garin mai suna Baban David ya bayyana cewa, an nada marigayin a matsayin shugaban al’ummar ne a ranar Asabar.

“Dukkanmu mun taru a gidansa da sanyin safiyar (Asabar) domin mu taya shi murna kan nadin da aka masa. Mun yi mamaki da sanyin safiyar yau (Lahadi) muka fara jin karar harbe-harbe.

“Mun ji tsoro kuma ba mu iya fitowa daga gidajenmu ba. Daga baya kuma aka shaida mana cewa ‘yan bindigar sun kashe shi a gaban matarsa da iyalansa.

“Mun tarar da gawarsa kwance a kasa. Matarsa ta shaida mana cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin gidansu ne inda suka harbe shi. Ba su dauki komai ba, ba su kuma sace kowa ba.”

A nasa bangaren, wani mazaunin garin mai suna Mallam Buhari ya bayyana cewa da sanyin safiyar ranar Lahadi fusatattun jama’a sun farmaki matsugunan Fulani da ke kusa, inda ya bayyana su a matsayin munafukai kuma ‘yan ta’adda.

Buhari ya ce yayin da suke barin yankin, an kai musu farmaki tare da kashe wasu daga cikinsu, ya kara da cewa: “A kan hanyarmu ta fitowa daga kauyen mun kirga gawarwaki hudu. Daga baya a kan hanyar daji, an ga gawarwakin wasu goma a jibge a kasa.”

A halin da ake ciki, an ce an baza ‘yan sanda a cikin al’umma domin tabbatar da doka da oda. Ko da al’amura sun koma daidai ga al’ummar, yawancin mazauna yankin sun kaurace wa yankin saboda fargabar abin da ka iya biyo baya.

Related posts

Leave a Comment