Kungiyar ha?in kan matasan Arewa ta yi tir gami da Allah wadai da yunkurin Kamfanin NNPC karkashin jagorancin Mele Kyari na mi?a kula da Matatun man fetur ga kasurgumin dan ta’adda Oweizide Ekpemupolo wanda aka fi sani da suna Tompolo.
Matasan na Arewa sun yi wannan gargadi ne a wani taron manema labarai da suka kira wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna.
Da ya ke jawabi a yayin taron mataimakin Kakakin ?ungiya na kasa Abdulsalam Mohammed Kazeem, yace kiran nasu ya zama wajibi duba da irin hatsarin dake tattare da mika al’amari mai muhimmanci irin wannan a hannun ?an ta’adda Tompolo.
“Hakika man fetur shine hanya ?aya tilo na samun arzikin Najeriya idan ya zamana har gwamnati za ta yi wannan ganganci na mi?a kula da bututu ga ?an ta’adda babu shakka an bu?e wata kofar barna da ba a san inda za ta tsaya ba.
Matasan sun yi gargadin cewa ba da wannan kwangila ga Tompolo za ta sanya sauran ‘yan ta’adda ganin cewa suna bisa daidai, inda ‘yan ta’adda irin su Nnamdi Kanu da Bello Turji su ma za su iya bayyana aniyar su ta neman kwangila kula da wasu muhimman abubuwa a Najeriya, wanda hakan ba karamin hatsari ba ne.
“Muna kira da babbar murya lallai da a dakatar da wannan shiri na mi?a kula da bututun mai ga Tompolo, ba kula da su ba gaba ?aya bai cancanci ya kusanci inda suke ba.
Kuma domin a dakile tunanin Matasa masu tasowa nan gaba da su guji shiga cikin ayyukan ta’addanci domin babu riba.
