Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Sojojin Najeriya sun kashe ?aya cikin manyan kwamandojin Iswap da wasu maya?a a wani farmaki a yankin arewa maso gabashi.
Sojojin sun ce sun kashe kwamandan mai suna Abubakar Danbuduma da maya?a 19, yayin da suka kwato tarin makamai masu yawa.
Rundunar sojin ta ce dakarunta sun kai harin ne a yankin Tafkin Chadi ta hanyar amfani da jiragen ya?i.
Abu ne mai wahala a iya tantance gaskiyar labarin. Amma wannan na zuwa a yayin da maya?an Iswap ke kar?e ikon wasu ?auyuka tana tilasta wa mutane biyan haraji
