Da Dumi-Dumi: Za A Fallasa Wadanda Suka Shirya Harin Jirgin Abuja – Fadar Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya tace nan bada jimawa ba, zata sanar da wa?anda suka ?auki nauyin kai harin Jirgin ?asan Abuja-Kaduna.

Gwamnatin ta kuma bayyana mummunan lamarin aka abinda ya bayyana ha?in gwiwa tsakanin Boko Haram da ?an Bindiga dake gudanar da harin su a yankin.Ministan Tsaro Manjo-Janar Bashir Magashi

Yace duk da Jami’an tsaro na yin bakin ?o?ari domin gano Dabar data kai harin, rahoto ta nuna cewa, ?ungiyar ?an bindigar tana ha?a hannu da wasu, yana mai kira ga ?an Najeriya dasu ha?a hannu da Gwamnati domin gano su.

Idan dai za’a tuna Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Jahar Kaduna ya bayyana cewar kai harin a Jirgin ?asa ?ungiyar Boko Haram ta ?auki nauyin kaishi, da suke aiki a tare da wasu ?an bindiga a Kaduna, Zamfara, da Sokoto, da Niger, da Kebbi.

Da suke maida jawabi bayan taron Majalisar Zartaswa, Ministan Tsaron Manjo-Janar Bashir Magashi dana Ya?a Labaru Alhaji Lai Mohammed sun bada tabbacin cewa tana kan gano lamarin.

Magashi a lokacin da yake maida jawabi akan ko Gwamnati ta gano wa?anda suke bayan kai harin, yace “dagaske, ina tunanin Hafsoshin Tsaro na bakin ?o?arin su domin gano wa?anda suke bayan kai hari, kuma zamu gaya maku wa?anda suka kai harin nan bada jimawa ba.

Related posts

Leave a Comment