Da Dumi-Dumi: Bam Ya Hallaka Sama Da Mutum 20 A Taraba

BASHIR ADAMU, JALINGO.

Wasu da ba a san ko su waye bane sun tayar da nakiya a Mashayar Burkutu a Kauyen Iware, dake Karamar Hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba.

Wani Shida daya gani da ido da baiso a anbaci sunansa ba yace, tashin nakiyar ya kashe a kalla mutane 20, tare da jikkata wasu mutane da dama, kana “tuni an garzaya da wadanda suka jikkata Karamin Asibitin Matakin Farko dake Iware, tare kai wasu Asibitin Kwararru da Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya dukkansu dake Jalingo.

Ya kuma kara da cewa, tuni Mutanen da suka tsira da rayukansu a wurin suka hallaka Matashin da suke zargi da dasa Nakiyar.

Kauyen Iware dai, na nesa ne da Kilo Mita 30 daga Jalingo Fadar Jihar Taraba, dake Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Duk kokarin da Wakilinmu na Jihar, Bashir Adamu, yayi domin jin ta bakin Kakakin Rundunar Yansandan Jihar Taraba, Abdullahi Usman, akan lamarin yaci tura.

Related posts

Leave a Comment