Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa abu ne mai wahala a yaki yan fashin daji saboda yanayin da suke kai farmaki.
Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a shirin gidan radiyo na Bond FM a karshen mako.
Ya ce gwamnati mai ci ta zuba ku?i sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, inda ya kara da cewa kokarin zai fi yin tasiri ne idan al’umman kasar suka mara wa kokarin da gwamnati ke yi baya.
Da yake martani ga shawarar Gwamna Nasir El-Rufai na yin hayar sojoji daga waje, Mohammed ya ce: “Ba za a iya kwatanta sojojin haya da rundunonin tsaronmu ba; yaki da yan fashi yana da matukar wahala ne saboda yanayin.
Ba za mu iya zuwa da karfi don tayar da su da bam ba idan ba haka ba za a kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba wadanda ke zama a kewaye da su, kuma bama so hakan ya faru.
“Idan muka kwaso sojojin haya domin su yaki ‘yan fashi, sai mu saka a zukatanmu cewa su yan haya ne kawai ba wai jami’an tsaronmu ba wadanda za su koma koina bayan kammala aikinsu.”
Ministan ya kuma roki ‘yan Najeriya da su hada hannu a yaki da yan fashin, cewa gwamnatin tarayya ba za ta iya yi ita kadai ba.
“Muna kuma rokon ‘yan Najeriya da su hada hannu a wannan yakin saboda suna da rawar ganin da za su taka a wajen magance wannan matsala ta rashin tsaro. Hakan ya kasance ne saboda wadannan miyagun da ake kira yan fashi suna zama ne a tsakaninmu; suna kuma hulda da mutane. “Su wa ke kai masu abinci? Bugu da kari, suma suna da ubannin gidan da suke haya.
Ya kamata mutane su dunga fallasa wadannan miyagu sannan ne za mu fara ganin sakamakon kokarin da gwamnati ke yi.
