Rahotanni daga Minna babban birnin jihar Neja na bayyana cewar Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Matane, ya tabbatar da kashe kananan yara shida bisa kuskure wanda jirgin ya?in sojin sama ya yi a jihar.
Sakataren gwamnatin na cewa sun gudanar da bincike don tabbatar da lamarin wanda ya faru a makon da ya shu?e. Ya ce kananan yaran sun rasa rayuwarsu ne yayin da jirgin ya?in ke aikin tarwatsa yan ta’adda a wasu sansanonin su dake cikin jihar.
” Lamarin ya afku bisa kuskure, gwamnatin Neja ta yi duba zuwa lamarin kuma tana cigaba da gudanar da bincike domin gano ainihin abun da ya faru.”
A cewar shugaban gamayyar ?ungiyoyin al’umma na Shiroro, Salis Sambo, jirgin ya?in ya yi kuskuren kashe yaran ne lokacin da yake kokarin jefa wa wasu yan ta’adda Bam, wa?an da suka gudu cikin ?auyen domin tsira.
Ya ce yaran da abun ya shafa suna kan hanyar su ta dawowa daga wurin debo ruwa, inda ya ?ara da cewa mutum hudu daga cikin su yan gida ?aya ne.
