Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Dauke Ango Da Amarya

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu sabbin ma’aurata bayan kashe jami’an sa-kai biyu a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke birnin Katsina. A cewar mazauna unguwar ‘yan bindigar sun far mu su ne da misalin ?aya da minti ashirin da biyar na dare, kuma sun shafe sa’a guda su na harbe-harbe. Sun shaida cewa ‘yan sa-kai sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma’auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu. Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci…

Read More

Da Dumi-Dumi: An Hallaka Gogarman ‘Yan Bindiga Abdulkarim Boss

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe wani kasurgumin ?an fashin daji Albdulkarim Boss da mutanansa 27 a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin ya?i ya yi a kan maboyarsu. Abdulkareem Lawal wanda aka fi sani da Abdulkareem Boss, an jima ana farautarsa kafin a hallaka shi a wannan lokaci. Hare-haren sama da sojojin suka kaddamar na zuwa ne kasa da mako guda da shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da manyan hafsoshin tsaron ?asar da su ka yi alkawarin kawo ?arshen matsalolin tsaron Najeriya. An hallaka ?an fashin…

Read More

IPOB Ce Ta Hallaka ‘Yan Sanda A Jihar Imo – Rundunar ‘Yan Sanda

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a Jihar Imo ta ce ‘yan bindigar da suka kashe jami’anta hu?u a harin ranar Juma’a mambobin ?ungiyar tsagerun inyamurai ne masu hankoron kafa Biafra (IPOB) ne. Wata sanarwa da kakakin rundunar na jihar Imo ya sanya wa hannu ta ce wasu mutum biyu da ake tsare da su a ofishin “yan sanda na Agwa – inda aka kai harin – sun tsere sakamakon harin. CSP Michael Abattam ya ce maharan sun afka wa ?ofar ginin ta hanyar amfani da motar ?iban yashi wato tifa, inda…

Read More

Mayakan Ansaru Na Auren ‘Yan Mata A Jihar Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga yankin Birnin Gwari a Jihar Kadunan na bayyana cewa ?an ?ungiyar Ansaru na ?ulla aure tsakanin ‘yan matan yankin da maya?anta. Irin wannan lamari dai ya faru a garin Tsohuwar Kuyallo, inda wasu ‘ya’yan ?ungiyar suka angwance da ‘yan matan garin a ranar Talata. Wani mazaunin yankin Birnin Gwari ya tabbatar wa BBC da ?aurin auren, inda ya ce ba sabon abu ba ne a yankin. Ya kara da cewa ko a watanni kimanin biyu da suka gabata maya?an ?ungiyar sun ha?a aure da wasu…

Read More

Kaduna: Mataimakin Shugaban ‘Yan Sanda Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Mataimakin Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriya da ke shugabantar sashe na 12 da ke Bauchi, Audu Madaki, ya tsira da ranshi amma ya samu raunuka daga harsashi a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai wa motarsa hari a kusa da garin Kwoi da ke Jihar Kaduna. An kai wannan hari ne ranar Talata a lokacin da AIG din yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Bauchi, tare da ma’aikatansa ba tare da motocin masu tsaronshi ba. Wasu majiyoyin tsaro wadanda ba su yarda a bayyana sunayensu…

Read More

Jirgin Abuja-Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sako Karin Mutum Biyar

‘Yan bindigar da suka sace fasinjoji a jirgin kasar da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din da ya gabata sun saki karin fasinjoji biyar. Hukumomin tsaro da gwamnatin kasar ba su tabbatar da sakin karin mutanen ba, amma gidan talbijin na Channels TV ya ambato mutumin da ke shiga tsakani domin sako fasinjojin Tukur Mamu yana cewa an saki mutanen ne a ranar Talata. Ya bayyana cewa mutanen da aka saka su ne: Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Mukthar Shu’aibu da Sidi…

Read More

Matsalar Tsaro: An Shawarci Buhari Ya Kori Monguno

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sanata Sani Musa mai wakiltar Neja ta gabas a majalisar dattawa ya bukaci Janar Babagana Monguno mai ritaya ya sauka daga mukaminsa ko kuma Shugaban ?asa ya kora shi. Sanata Sani Musa yana mai cewa akwai bukatar Hadimin shugaban kasar ya yi murabus saboda gazawarsa ta fito fili karara. Kwanakin baya aka ji ‘yan ta’adda sun fito suna barazanar za su dauke Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da Mai girma Muhammadu Buhari. Da aka yi hira da Nasir El-Rufai,…

Read More

Kano: Ana Tuhumar ‘Yan Sintiri Da Kisan Malamin Allo

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewa ana zargin ‘yan sintiri da kashe wani malamin makarantar allo a unguwar Dabai, da ke karamar hukumar Gwale ta Jihar . Shi dai Malam Musa Mai-Almajirai, sanannen malamin Qur’ani ne a unguwar, inda yake da ?aruruwan almajirai. Ana zargin ‘yan sintirin da yi wa malamin dukan tsiya a ofishinsu bayan da aka kai shi can bisa zargin da wata mata ta yi masa na yunkurin satar yaro. An ruwaito cewa ?an malamin, Ibrahim ya sheda cewa, ”Mahaifin nasa yana tafiya…

Read More

Filato: Mutum 18 Sun Mutu A Gwabzawar ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Sa Kai

Labarin dake shigo mana daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewa Mutum 16 da ake zargin ‘yan bindiga ne da ‘yan vigilante biyu sun mutu a bata-kashi tsakanin bangarorin biyu a garin Bangalala da ke karamar hukumar Wase a Jihar Filato. Bangalala na da nisan kilomita 100 daga garin Wase, hedikwatar karamar hukumar. Kauyukan da ke Wase na fama da hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane da shanu, abin da ya tilastawa mutane da dama tserewa daga gidajensu. Wasu jaridun Najeriya sun rawaito cewa lamarin ya faru a kokarin…

Read More

An Yi Nasarar Cafke Wa?anda Suka Kitsa Harin Kurkukun Kuje

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke wasu mutane hudu da ake zargin na kwarmata bayanan sirri ga ‘yan bindiga a babban birnin tarayya. Jaridar PRNigeria ta rawaito wata majiya mai karfi ta hukumar leken asiri ta kasa da ke tabbatar da kamen. Jaridar ta ce an cafke mutanen tare da wasu na’urori da makamai da tsoffin wayoyin hannu da basa amfani da intanet. Majiyar da ke cikin ayarin mutanen da suka yi kamen na cewa, ana ci gaba da bincike cikin sirri domin gano…

Read More

‘Yan Bindiga Na Hijira Zuwa Jihar Nasarawa – Gwamna Sule

Labarin dake shigo mana daga Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewa gwamnan Jihar Abdullahi Sule ya bayyana damuwa game da yadda gungun ‘yan fashin daji ke tururuwa zuwa jiharsa bayan koro su daga ma?wabtan jihohi. Gwamna Abdullahi Sule ya ce jami’an tsaro sun lura da ?aruwar ‘yan bindiga a ?aramar hukumar Karu, wadda ke da nisan ?asa da kilomita 30 daga Abuja babban birnin ?asar. “Mun lura da tarin ‘yan fashin nan da aka koro daga jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Kebbi musamman a yankunan Rugan…

Read More

Tsaro: Gumi Ya Soki Gwamnatin Tarayya Kan Sukar Rahoton BBC

Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya soki gwamnatin tarayya kan barazanar da ta yi na hukunta kafafen watsa labarai game da wallafa rahotanni kan rashin tsaro da ya dade yana damun kasar. A ranar Alhamis, Ministan Labarai da Al’addu, Lai Mohammed ya ce za a hukunta BBC da Trust TV saboda bidiyo da suka yi na yan bindiga dake azabtar da mutane a sashin Arewa maso yammacin kasar. A martaninsa, malamin addinin musuluncin ya ce gwamnati na kokarin rufe bakin kafafen watsa labarai su daina bayyana gazawarta da…

Read More

Taraba: Rashin Aiki Yi Ne Silar Matsalar Tsaro – Sarkin Bakundi

BASHIR ADAMU, JALINGO. Mai-martaba Sarkin Bakundi, dake Gundumar Dali, Karamar Hukumar Bali na Jihar Taraba, Alhaji Kabiru Muhammad Gidado, a zantawanshi da manema Labarai a Fadanshi yace ko shakka babu, rashin ayyukanyi musamman ga Matasa na daga cikin abubuwan dake assasa fitittinu a Kasannan. Yana maijan hankalin Matasa dasu gujewa zama cikin jahilci “Na horeku, ku matasan Masarauta na Bakundi, ku gujewa zama cikin jahilci, ku tsunduma kanku dumu-dumu cikin niman Ilimin Addini dana Zamani, domin jahilci mugun ciwone”. Sarki Kabir ya kuma roki Gwamnatin Tarayya dana Jihar Taraba da…

Read More

Taraba: Kuru-Jibu Ya Jinjinawa Gwamnati Wajen Samar Da Tsaro

BASHIR ADAMU, JALINGO Mai Martaba Kuru- Jibu, dake Karamar Hukumar Bali, Jihar Taraba, Alhaji Mahmud Adamu ya nuna matukar farin cikinsa kan samun zaman lafiya da sukayi ta yanda suke iya shiga gonakin su noma. Kuru-Jibu, Mahmud Adamu ya baiyana hakane lokacin da yake ganawa da manema Labarai a Fadanshi. Mahmud Adamu na mai cewa a baya dai masu garkuwa da Mutane domin kudin fansa da barayin daji sun addabi yankunansu, ta yanda babu wani mahalukin daya isa yaje gonanshi aiki, ko kiwo, inda tun a farko suka aike da…

Read More

Tsaro: Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Sana’ar Karuwanci

Rahoton dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewa gwamnatin Jihar za ta haramta karuwanci a babban birnin jihar a matsayin wani mataki na magance matsalar rashin tsaro. Kaltum Rufai, Sakatariyar dindindin a ma’aikatar mata da ayyukan cigaba na jihar ce ta bayyana hakan cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, yayi da ita a Minna. Ms Rufai ta ce gwamnati ta san da wannan lamarin mara dadi wanda ka iya zuzuta kallubalen tsaro da ake fama da shi a jihar. Ta ce…

Read More

Garkuwa Da Mutane: Kashe Mu Raba Muke Da Jami’an Gwamnati – Shugaban ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa wani ?asurgumin ?an bindiga mai satar mutane a Jihar ya ce matsalar rashin tsaro na ?ara ta’azzara ne a arewacin ?asar saboda an mayar da lamarin na neman ku?i. Abu Sani wanda shi ne ya jagoranci sace ?an matan sakandaren gwamnati ta garin Jenge?e a bara, ya fa?i hakan ne a wani shiri na musamman na binciken ?wa?waf da BBC ta gudanar kan ayyukan ?an bindigar. “An mayar da abin neman ku?i a wannan ?angare, kowa ku?i yake nema,shi ya…

Read More

Adamawa: An Damke Matar Da Ake Zargi Da Kashe Mijinta

A yanzu haka rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa tana tsare da wata mata mai suna Caroline Barka ‘yar shekaru 28 da haihuwa bisa zarginta da dabawa mijinta wuka wanda kuma yayi sandiyar tafiyarsa lahira. Runduna ta baiyyana hakane a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan SP Suleiman Yahaya Nguroje wanda aka rabawa manema labarai a Yola. Sanarwa tace bincike ya nuna cewa matar tana zaune a Anguwan Tamiya dake cikin karamar hukumar Madagali a jahar Adamawa inda ta cakawa mijinta mai suna Barka Dauda dan shekaru 38 da…

Read More

Muna Fama Da Karancin Wurin Ajiye Tubabbun Boko Haram – Rundunar Soji

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Hukumomin tsaro sun ce sun fara rasa wuraren da za su ajiye maya?an Boko Haram da suka mi?a wuya. Babban jami’in soja Manjo Janar Chris Musa ya ce a yayin da mi?a wuyan da maya?an Boko Haram ?in ke yi yake taimakawa wajen shawo kan rikicin da ya addabi yankin, a gefe guda kuma babu isassun wuraren ajiye su. Babban janar ?in ya ce zuwa yanzu akwai maya?an da suka yi saranda kuma suke jiran bin matakan sauya musu tunani,…

Read More

Kashi 80 Na Wadanda Aka Kashe A Najeriya ‘Yan Arewa Ne – Bincike

Wata kididdiga game da sha’anin tsaro a Najeriya ya nuna cewa kashi 75.6 na mutanen da aka kashe sakamakon hare-hare a watan Yuni a arewacin kasar suke. Sabuwar kididdigar, wadda kamfanin Beacon Consulting Limited da ke nazari kan harkokin tsaro ya fitar a wannan watan, ta bayyana cewa an kai hari 338 a fadin kasar a watan na Yuni lamarin da ya kai ga sace mutum 651. Kazalika an kashe “mutum 765. Wannan lamari ya faru ne a kananan hukumomi 185 da ke jihohi 36 da Abuja, babban birnin kasar.”…

Read More

Adamawa: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yi Babban Kamu

Rundunan yan sandan jihar Adamawa tayi nasarar cafke mutane goma sha uku wadanda ake zargi da aikata lafika daban daban a fadin jihar ta Adamawa. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sikiru Kayode Akande ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatarwa manema labari wadanda ake zargin a shelkwatan Rundunar dake Yola. Kwamisihinan ‘yan sandan ya kara da cewar Rundunar ta kuma kama daya daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo wadanda suka gudu daga gidan yari kuje a Abuja bayan hari da aka kai a gidan yarin. Wanda aka…

Read More