Jirgin Abuja-Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sako Karin Mutum Biyar

‘Yan bindigar da suka sace fasinjoji a jirgin kasar da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din da ya gabata sun saki karin fasinjoji biyar.

Hukumomin tsaro da gwamnatin kasar ba su tabbatar da sakin karin mutanen ba, amma gidan talbijin na Channels TV ya ambato mutumin da ke shiga tsakani domin sako fasinjojin Tukur Mamu yana cewa an saki mutanen ne a ranar Talata.

Ya bayyana cewa mutanen da aka saka su ne: Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.

Babu bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin a saki fasinjojin.

Related posts

Leave a Comment