Kano: Ana Tuhumar ‘Yan Sintiri Da Kisan Malamin Allo

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewa ana zargin ‘yan sintiri da kashe wani malamin makarantar allo a unguwar Dabai, da ke karamar hukumar Gwale ta Jihar .

Shi dai Malam Musa Mai-Almajirai, sanannen malamin Qur’ani ne a unguwar, inda yake da ?aruruwan almajirai.

Ana zargin ‘yan sintirin da yi wa malamin dukan tsiya a ofishinsu bayan da aka kai shi can bisa zargin da wata mata ta yi masa na yunkurin satar yaro.

An ruwaito cewa ?an malamin, Ibrahim ya sheda cewa, ”Mahaifin nasa yana tafiya ne sai ya ji kukan jariri sabuwar haihuwa a wata bola.

Sai ya je ya dauki yaron, sai kawai wata mata ta yi masa ihu, tana ce masa barawon yaro.”

”Kururuwar da matar ta yi ce ta janyo ‘yan sintirin da sauran jama’ar unguwar suka rufe shi da duka,”

Ya kara da cewa, ”Daga nan sai suka tafi da shi ofishinsu suka ci gaba da dukansa. Daga baya ya fadi ya suma.”

Ya ce,” Bayan da wasu ‘yan unguwar suka gane shi sai suka garzaya da shi asibiti, inda ya cika a hanya.”

Related posts

Leave a Comment