BASHIR ADAMU, JALINGO
Mai Martaba Kuru- Jibu, dake Karamar Hukumar Bali, Jihar Taraba, Alhaji Mahmud Adamu ya nuna matukar farin cikinsa kan samun zaman lafiya da sukayi ta yanda suke iya shiga gonakin su noma.
Kuru-Jibu, Mahmud Adamu ya baiyana hakane lokacin da yake ganawa da manema Labarai a Fadanshi.
Mahmud Adamu na mai cewa a baya dai masu garkuwa da Mutane domin kudin fansa da barayin daji sun addabi yankunansu, ta yanda babu wani mahalukin daya isa yaje gonanshi aiki, ko kiwo, inda tun a farko suka aike da kokensu ga Gwamnatin Jihar Taraba dana Tarayya, domin daukan matakin gaggawa, inda nan take sukayi abin a yaba na tura Jami’an Tsaron hadin guyiwa, da suka fatattaki Yan ta’addan ta Sama data Kasa da hakan ya tabbatar musu da tsaro a yankin.
“Karamar Hukumar mu ta Bali, ta samo asaline daga Kwararrafa, inda Kakannin mu suka fito, da yin zango a Wurbo izuwa Bali na yanzu. Sunan ‘Bali’, ya samu ne daga sunan Baa- Ali.”
“Yan ta’adda na amfani da Dajinmu ne sakamakon manyan duwatsu, da itatuwan (Kurmi) da muke dashi, inda suka maidashi wurin fakewansu, suna aikata ayyukan ta’addancin, don Bali tayi iyaka da Gunduma ta Karamar Hukumar Gassol. Yan ta’addan na fitowa a daji daga Jos din Jihar Plateau su shigo ta Gunduma su samu fakewa a dajinmu na Bali, sukan hana Mutanen mu Noma da sauran ayyuka, amma yanzu Alhamdulillah, mun godewa Gwamnatin Jihar Taraba dana Tarayya bisa daukin gaggawa da suka kawomana wurin fatatattakan wadan nan azzalumai Yan’ ta’adda, da suka hanamu sikit, yanzu haka da nike magana daku mun cigaba da noman mu, mun gode Allah “.
Mai Martaban, ya kuma gargadi Manoma dasu gujewa gaggawan siyarda abincin da suka noma, a cewanshi hakan babu alfanu, domin akarshe sukan koma suna siyan na cinsu a wurin Yan kasuwa da tsada.
Ya kuma roki Shuwagabanni a kowani mataki da suyi adalci kana “Al’ummah anasu bangaren da su cigaba da cudanya da juna cikin aminci da lumana a dukkanin lamuranku “ku gujewa cusa ban-bancin Addini, Kabilanci ko yanki”.
Mai-martaba, Alhaji Abubakar Mahmud Adamu, ya ankarar da Kwamitin da sukayi don wayarwa Matasa kai don sanin muhimmancin mallakan Katin Zabe da zaben Shuwagabanni nagari.
A wani batu na dakile dumaman yanayi da kwararowan hamada, Mahmud Adamu yace “a bangaren Masarautan mu, shiri ya kammala ta yanda duk wani mutum da yashigo yankinmu, a kasa, keke, mashin ko mota, sai mun tsaidashi ko ita, mun basu tsirai na itatuwa su shuka, mun aikewa sauran masu ruwa da tsaki da abun ya shafa, domin amincewansu, da wannan tsarin na tabbata zamu maye guraben itatuwan da ake cirewa a Kasanmu”.
