Adamawa: An Damke Matar Da Ake Zargi Da Kashe Mijinta

A yanzu haka rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa tana tsare da wata mata mai suna Caroline Barka ‘yar shekaru 28 da haihuwa bisa zarginta da dabawa mijinta wuka wanda kuma yayi sandiyar tafiyarsa lahira.

Runduna ta baiyyana hakane a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan SP Suleiman Yahaya Nguroje wanda aka rabawa manema labarai a Yola.

Sanarwa tace bincike ya nuna cewa matar tana zaune a Anguwan Tamiya dake cikin karamar hukumar Madagali a jahar Adamawa inda ta cakawa mijinta mai suna Barka Dauda dan shekaru 38 da haihuwa wuka biyo bayan rashin jituwa da ya shiga tsakaninsu.

Lamarin dai ya farune a lokacin da maigidan nata ya dawo da daddare a buge wanda hakan yasa ya fadi akan yarsu yar ahekara daya da haihuwa a lokacin tana kwance akan gado. Kuma matar tace mijin nata baya bata abinda ya kamata yayi mata a matsayin matarsa.

Acewar sanarwan da kakaki rundunan ‘yan sandan ya fitar dai na cewa suna cigaba bincike kan lamarin kuma da zaran sun kamma bincike zasu gurfanar da ita gaban kotu domin ta fuskanci Shari’a.

Related posts

Leave a Comment