Labarin dake shigo mana daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewa Mutum 16 da ake zargin ‘yan bindiga ne da ‘yan vigilante biyu sun mutu a bata-kashi tsakanin bangarorin biyu a garin Bangalala da ke karamar hukumar Wase a Jihar Filato.
Bangalala na da nisan kilomita 100 daga garin Wase, hedikwatar karamar hukumar.
Kauyukan da ke Wase na fama da hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane da shanu, abin da ya tilastawa mutane da dama tserewa daga gidajensu.
Wasu jaridun Najeriya sun rawaito cewa lamarin ya faru a kokarin jami’an sa-kai na vigilante kwato kauyen Bangalala da ke hannun ‘yan bindiga tsawon watanni.
Mazaunan yankunan dai sun tabbatar da wannan al’amari, sai dai jami’an tsaro ba su tsokaci ba kawo yanzu.
