Rahoton dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewa gwamnatin Jihar za ta haramta karuwanci a babban birnin jihar a matsayin wani mataki na magance matsalar rashin tsaro.
Kaltum Rufai, Sakatariyar dindindin a ma’aikatar mata da ayyukan cigaba na jihar ce ta bayyana hakan cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, yayi da ita a Minna.
Ms Rufai ta ce gwamnati ta san da wannan lamarin mara dadi wanda ka iya zuzuta kallubalen tsaro da ake fama da shi a jihar. Ta ce akwai dokoki na jihar da suka hana hakan, tana mai cewa gwamnati za ta yi bincike da nufin kawo karshen mummunan abin.
“Yanzu da kun kawo koke kan lamarin, gwamnati za ta dauki mataki. “Da kai na zan tafi in ga sakataren gwamnatin jiha don tattauna batun da yadda za a warware shi,” in ji ta.
Binciken da NAN ta yi a Minna, ya nuna cewa yan mata da mata sukan fara harkar ta su ne daga karfe 7 na yamma zuwa 12 na dare.
