Mayakan Ansaru Na Auren ‘Yan Mata A Jihar Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga yankin Birnin Gwari a Jihar Kadunan na bayyana cewa ?an ?ungiyar Ansaru na ?ulla aure tsakanin ‘yan matan yankin da maya?anta.

Irin wannan lamari dai ya faru a garin Tsohuwar Kuyallo, inda wasu ‘ya’yan ?ungiyar suka angwance da ‘yan matan garin a ranar Talata.

Wani mazaunin yankin Birnin Gwari ya tabbatar wa BBC da ?aurin auren, inda ya ce ba sabon abu ba ne a yankin.

Ya kara da cewa ko a watanni kimanin biyu da suka gabata maya?an ?ungiyar sun ha?a aure da wasu ‘yan mata biyu a yankin.

BBC ta tuntu?i rundunar ?an sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna game da wannan lamari, inda ta ce tana gudanar da bincike a kai.

Sai dai masana harkokin tsaro kamar Muhammad Kabir Isa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, na ganin sakacin gwamnati ne ta fuskar tsaron ya sa kungiyar ke amfani da irin wadannan hanyoyi domin samun shiga tsakanin al’umma, har abin ya kai ga hada zuri’a.

“Yanzu idan suka yi aure cikin jama’a, yaran gidan ko mazan da ke ciki sun zama nasu, wa?annan duk dabaru ne na samun mabiya da mutanen da za su dauki akida da ra’ayoyinsu,” in ji Muhammad Kabir.

Related posts

Leave a Comment