IPOB Ce Ta Hallaka ‘Yan Sanda A Jihar Imo – Rundunar ‘Yan Sanda

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a Jihar Imo ta ce ‘yan bindigar da suka kashe jami’anta hu?u a harin ranar Juma’a mambobin ?ungiyar tsagerun inyamurai ne masu hankoron kafa Biafra (IPOB) ne.

Wata sanarwa da kakakin rundunar na jihar Imo ya sanya wa hannu ta ce wasu mutum biyu da ake tsare da su a ofishin “yan sanda na Agwa – inda aka kai harin – sun tsere sakamakon harin.

CSP Michael Abattam ya ce maharan sun afka wa ?ofar ginin ta hanyar amfani da motar ?iban yashi wato tifa, inda suka karya ?yauren tare da jefa abubuwan fashewa.

Wata majiya ta bayyana cewa cikin wa?anda aka kashe akwai maza biyu da mata biyu, amma sanarwar ta ce wata mota ce ta kama da wuta a farfajiyar kuma an kashe ta “ba tare da ginin ya kama ba”.

Majiyar ta ?ara da cewa ?aya daga
cikin wa?anda lamarin ya ritsa da su bai wuce mako biyu da fara aiki da rundunar ba.

Related posts

Leave a Comment