BASHIR ADAMU, JALINGO.
Mai-martaba Sarkin Bakundi, dake Gundumar Dali, Karamar Hukumar Bali na Jihar Taraba, Alhaji Kabiru Muhammad Gidado, a zantawanshi da manema Labarai a Fadanshi yace ko shakka babu, rashin ayyukanyi musamman ga Matasa na daga cikin abubuwan dake assasa fitittinu a Kasannan. Yana maijan hankalin Matasa dasu gujewa zama cikin jahilci “Na horeku, ku matasan Masarauta na Bakundi, ku gujewa zama cikin jahilci, ku tsunduma kanku dumu-dumu cikin niman Ilimin Addini dana Zamani, domin jahilci mugun ciwone”.
Sarki Kabir ya kuma roki Gwamnatin Tarayya dana Jihar Taraba da su taimaka wurin kawowa Yankin Taraba ta Tsakiya wutan lantarki, a cewan Sarkin hakan ko shakka babu zai taimaka musu matuka wurin farfado da tattalin arzikin yankinsu “Matasa, Maza, Mata, Manya da Yara zasu sami daman yin sana’oi daban daban, kuma Attajirai zasu samu zarafin kafa Kamfanoni, hakan zaisa hada-hadan kasuwanci ya habaka a yankinmu, kuma ya sanya komai ya dai-daita”.
Muhammad Gidado ya godewa Gwamnatin Jihar Taraba, kan jajircewa da takeyi wurin kawo zaman lafiya da kuma yanda aikin hanyar Panmanga zuwa Dakka ke tafiya. Tare da Rokon Gwamna Darius Ishiaku daya gyara musu Babban Asibitin Gwamnatin Jiha ta Bali wato (General Hospital, Bali) da a yanzu haka yake cikin mummunan yanayi, wanda Sarkin ya tabbatar da cewa gyaran zai sauwakawa Al’ummah wahal-halun da suke fama dashi wurin neman lafiya.
