Muna Fama Da Karancin Wurin Ajiye Tubabbun Boko Haram – Rundunar Soji

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Hukumomin tsaro sun ce sun fara rasa wuraren da za su ajiye maya?an Boko Haram da suka mi?a wuya.

Babban jami’in soja Manjo Janar Chris Musa ya ce a yayin da mi?a wuyan da maya?an Boko Haram ?in ke yi yake taimakawa wajen shawo kan rikicin da ya addabi yankin, a gefe guda kuma babu isassun wuraren ajiye su.

Babban janar ?in ya ce zuwa yanzu akwai maya?an da suka yi saranda kuma suke jiran bin matakan sauya musu tunani, amma ba su da wajen ajiye su.

Wuraren ajiye mutanen sun cika ma?il – kuma a yanzu hukumomi suna duba yiwuwar gina wasu.

Matakan sauyawa da gyara tunani na cikin ?o?arin da gwamnatin Najeriya ke yi don kawo ?arshen ayyukan masu i?irarin jihadi, musamman a arewa maso gabashin ?asar.

Majalisar ?inkin Duniya ta yi ?iyasin cewa kusan mutum 350,000 ne suka mutu a rikici tsakanin ?ungiyar Boko Haram da rundunar sojin ?asar cikin shekara 12. Amma adadin ka iya fin haka.

Janar Chris Musa ya ce wani babban ?alubalen shi ne yadda suke samun matsalar mayar da ?an gudun hijira matsugunansu.

Related posts

Leave a Comment