Matsalar Tsaro: An Shawarci Buhari Ya Kori Monguno

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sanata Sani Musa mai wakiltar Neja ta gabas a majalisar dattawa ya bukaci Janar Babagana Monguno mai ritaya ya sauka daga mukaminsa ko kuma Shugaban ?asa ya kora shi.

Sanata Sani Musa yana mai cewa akwai bukatar Hadimin shugaban kasar ya yi murabus saboda gazawarsa ta fito fili karara.

Kwanakin baya aka ji ‘yan ta’adda sun fito suna barazanar za su dauke Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da Mai girma Muhammadu Buhari. Da aka yi hira da Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa shi ya fadawa shugaban kasar cewa rayuwarsa na cikin barazana, a lokacin sam bai da labari.

Da ake hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, Sanatan yace tun da Hadimin ya gaza ankarar da shugaban kasa, bai dace ya cigaba da aiki ba. Jigon na APC yake cewa hirar da aka yi da Gwamna El-Rufai ya nuna shugaba Buhari bai san halin da ake ciki ba, kuma hakan ya isa babban laifi.

Related posts

Leave a Comment