Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya soki gwamnatin tarayya kan barazanar da ta yi na hukunta kafafen watsa labarai game da wallafa rahotanni kan rashin tsaro da ya dade yana damun kasar.
A ranar Alhamis, Ministan Labarai da Al’addu, Lai Mohammed ya ce za a hukunta BBC da Trust TV saboda bidiyo da suka yi na yan bindiga dake azabtar da mutane a sashin Arewa maso yammacin kasar.
A martaninsa, malamin addinin musuluncin ya ce gwamnati na kokarin rufe bakin kafafen watsa labarai su daina bayyana gazawarta da kawar da hankulan mutane daga rashawa na kashe kudi a bangaren tsaro.
Ya jinjinawa kafafen watsa labaran na gida da kasashen waje da suka nuna jarumta wurin wallafa rahoto kan tabarbarewar tsaro a yankin. “Abin da ke faruwa a Najeriya yau musamman arewa maso yamma kamar yadda BBC ta yi rahoto yaki na kabilanci ne da ramuwar gayya saboda gazawar gwamnati ta magance rashin adalci da tun farko ake yi wa fulani,”
“Me ka ke tsammani daga al’umma (fulani) da aka bari cikin jahilci a lokacin da bata gari daga gwamnati da waje suka sace musu abin da rayuwarsu ta dogara a kai (shanu) ba kuma tare da an musu adalci ba.
