Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke wasu mutane hudu da ake zargin na kwarmata bayanan sirri ga ‘yan bindiga a babban birnin tarayya.
Jaridar PRNigeria ta rawaito wata majiya mai karfi ta hukumar leken asiri ta kasa da ke tabbatar da kamen.
Jaridar ta ce an cafke mutanen tare da wasu na’urori da makamai da tsoffin wayoyin hannu da basa amfani da intanet.
Majiyar da ke cikin ayarin mutanen da suka yi kamen na cewa, ana ci gaba da bincike cikin sirri domin gano shugabanninsu da masu daukar nauyinsu.
Jaridar ta kuma rawaito cewa hukumar tsaro ta Najeriya na tattara bayanan sirri domin gano masu hannu a matsalolin tsaro da hare-haren da ake kitsawa.
