Rahotanni dake shigo mana yanzu daga birnin Kano na bayyana cewar wasu gungun Matasa sun hallaka Matashi Muhammad Suleman a daren jiya sannan suka yi awon gaba da wayarshi. Rundunar yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar matashin mai suna Muhammad Suleman da ake zargin wasu Matasa suka kashe tare da kwace masa waya. Yan sandan sun ce an kashe matashin ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida tare da iyalinsa matasan suka tasar masa a kan titiun Yahaya Gusau a dare jiya Rundunar ‘Yan…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Tsaro: An Toshe Layukan Sadarwa A Jihar Sokoto
Rahotanni dake shigo mana yanzu daga Jihar Sokoto na bayyana cewar an toshe layukan sadarwa a jihar fiye da mako biyu bayan an toshe hanyoyin sadarwar a jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar. Gwamnatin jihar ta tabbatarwa BBC da matakin, inda kakakin gwamnan jihar Muhammad Bello ya ce an toshe layukan ne a ?ananan hukumomi 14 na jihar. Wasu mutanen jihar sun ce idan an kira layukan MTN ba a kamawa, wasu kuma sun ce matsalar ta shafi har da masu amfani da layin Airtel. Matakin toshe layukan na…
Read MoreAdamawa: Kimanin Mutum 2000 Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yi Nasarar Cafkewa A Bana
Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace tayi nasaran kama mutane dubu daya da dari daya da tamanin da hudu tun daga ran 11-1-2021 zuwa yanzu bisa zarginsu da aikata laifuka daban daban a fadin jahar Adamawa. Kwamishina yan sandan jahar Adamawa CP Aliyu Adamu Alhaji ne ya baiyana haka a lokacin da yake gabatarwa manema labarai wadanda ake zargin a shelkwatar rundunàn dake yola. Kwamishinan yace tun da ya fara aiki a matsayin kwamishinan yan sanda a jahar ta Adamawa rundunan ta nasara sosai wajen daki aiyukan bata gari a…
Read MoreSamar Da Tsaro Nauyi Ne Akan Kowa – Shugaban Majalisa
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya yi kira ga yan Najeriya kada su bar gwamnatin tarayya ka?ai wajen ya?i da matsalar tsaro, samar da tsaro nauyi ne dake akan kowa. Da yake jawabi a Iyin-Ekiti, jihar Ekiti, Lawan ya bukaci yan Najeriya su ?auki matsalar da muhimmanci kuma su ?auka kowa na da rawar da zai iya takawa wajen shawo kan matsalar. A cewar Kamfanin dillancin labarai, NAN, Sanata Lawan ya ziyarci Iyin-Ekiti ne bisa sarautar da basaraken Iyin-Ekiti, Adeniyi Ajakaye,…
Read MoreKogi: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Cikin Majami’a
Rahotanni daga Lokoja babban birnin Jihar Kogi na bayyana cewar Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne sun kai hari kan wani coci a jihar Kogi, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu masu ibada guda uku. Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a Cocin ECWA da ke Okedayo na garin Kabba, hedkwatar karamar Hukumar Kabba Bunu ta Jihar Kogi. Lamarin ya faru duk da cewa Gwamna Yahaya Bello ya bayyana jihar a matsayin mafi aminci a Najeriya. READ ALSO ‘Yan…
Read MoreSokoto: ‘Yan Bindiga Sun Kai Harin Ramuwar Gayya
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu gungun Yan bindiga sun kai sabon hari wani ?auye a ?aramar hukumar Tangaza, jihar Sokoto, inda suka hallaka mutum shida, da raunata wasu da dama. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki ?auyen, wanda mafi yawancin mutanen cikinsa mafarauta ne, da sanyin safiyar ranar Lahadi. Kuma yan bindigan sun kai harin ne dai-dai lokacin da mafi yawan mazan garin sun fita sana’arsu ta farauta. Sai dai babu tabbacin cewa ko harin miyagun yana da ala?a da kashe yan bindiga…
Read MoreRundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Ta Yi Wawan Kamu
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta bayyana cewa ta dam?e gaggan masu laifi har 25 tare da makamai tsakanin watan Agusta da Satumba. Kakakin Ya?a Labarai na ‘Yan Sandan Kaduna, Muhammad Jalige ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, a lokacin da ya ke wa manema labarai bajekolin masu laifin, a hedikwatar ‘yan sandan jihar, a Kaduna. Ya ce an kama su ne bayan sun aikata muggan laifuka da su ka ha?a da fashi da makami, kisan kai, garkuwa da mutane, ayyukan ?ungiyoyin asiri,…
Read MoreBabu Ranar Bude Layukan Sadarwa A Zamfara – Matawalle
Rahotanni daga birnin Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Bello Muhammad, Matawallen Maradun, ya ce babu ranar bu?e layukan sadarwa a jiharsa. A ranar juma’a wa’adin da gwamnan ya ?iba na bu?e layukan ya cika, kuma a hirarsa da BBC ya ce babu ranar dawo da layukan sadarwar a jihar. “Dole mu tsawaita don burinmu tabbatar da tsaron al’ummarmu,” in ji gwamna Matawalle. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da jami’an tsaro, kuma makomar tattaunawar ce za ta tantance lokacin da za a bu?e…
Read MoreKimanin ‘Yan Bindiga 300 Suka Shiga Hannu Cikin Watan Agusta A Jihar Neja
Rahotanni daga birnin Mina na Jihar Neja na bayyana cewar ?an sanda sun kama wasu mutum 259 da ake zargi da fashin daji da fya?e da garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a jihar cikin watan Agusta. Kwamishinan ?an sanda a jihar, Mista Monday Kuryas ya shaida wa kamfanin dillancin labari na NAN cewa an aikata laifuka a kananan hukumomi 25 na jihar. Ya bayyana cewa rundunar ?an sanda ta gano bindigogi da harsasai a hannun masu laifin. Mista Monday ya ce cikin mutanen 259 da ake zargi, an…
Read MoreKaduna: Sojoji Sun Ceto Sojan Da Aka Sace A Kwalejin NDA
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto Manjo Datong, sojan da ?an bindiga suka sace a harin da suka kai kwalejin koyon aikin soja ta NDA a Kaduna a watan da ya gabata. Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a ta ce an ceto sojan ne bayan musayar wuta da ?an bindiga tare da tarwatsa sansaninsu da suke tsare da jami’in sojan a yankin Afaka- Birnin Gwari. Sanarwar ta kuma ce ?an bindiga da dama ne aka kashe a farmakin da sojojin suka kai tare da taimakon…
Read MoreBauchi: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Masu Satar Mutane Da Mota
Kwamishinan Yan’sanda na Jihar Bauchi Sylvester Abiodun Alabi, ya ja hankalin iyaye kan yayansu, tare da gurfanar da wadanda suka shahara ta wajen garkuwa da mutane tare da satar motoci a cikin garin Bauchi da kewaye. Kwamishinan da yake ma manema labarai bayanin nasarorin da hukumar ta samu na damke masu aikata laifuffuka dabam dabam a kokuwar cikin garin Bauchi. Abiodun Alabi, Yace hukumar ta himmatu ne tare da samun bayanai daga sassan cikin garin tare da kai sumame a lungu da sako da jamianta suke kai wa lokaci zuwa…
Read MoreKaduna: An Yi Nasarar Damke Makasan Abdulkareem Na’Allah
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Rundunar ‘yan Sandan jihar ta yi nasarar kama wasu mutane 2 da ake zargin su na da masaniya a kan kisan Abdulkareem Na’Allah, dan Sanata Bala Ibn Na’Allah mai shekaru 36. Kamar yadda rahotanni suka bayyana, kwanaki kadan da suka gabata kenan da kama su. A ranar 29 ga watan Augustan 2021 aka tsinci gawar Abdulkareem, babban dan sanatan a dakin sa da ke Malali GRA a Kaduna. Sai dai babu kwararan bayanai a kan wadanda aka kama amma dai shekarun su 20…
Read MoreBoko Haram Sun Bude Sansani A Jihar Kaduna – DSS
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta nemi hukumomin tsaro a Kaduna da su kasance cikin shirin ko ta kwana kan yiwuwar kai hare-hare, a sassa daban daban na fa?in ?asar. Sanarwar ta bayyana cewa shugabanni da dakarun kungiyar ‘yan ta’adda na Boko Haram sun koma wani daji a Kudancin Kaduna bayan barin su Dajin Sambisa. A cikin wata sanarwa da jaridar Peoples Gazette ta gani, an ce yan ta’addan sun kaura daga dajin Sambisa a jihar Borno zuwa dajin Rijana da…
Read MoreYobe: Mutane Da Dama Sun Mutu Dalilin Aman Wutan Jiragen Yaki
Wani jirgin yaki ba a tantance daga ina yake ba ya yi aman wuta a yankin kauyen Buhari da ke karamar Yunusari a jihar Yobe da safiyar Laraba, inda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama. Al’ummar garin sun ce shaida wa BBC cewa sun wayi gari ne da ganin jiragen yaki har uku suna shawagi a sararin samaniyar garin nasu. Daga bisani daya daga cikin jiragen ya yi aman wuta kan wani bangaren garin, kamar yadda wani da ‘yan uwansa suka mutu a lamarin ya shaida wa BBC.…
Read MoreBorno: Tsohon Kwamandan Boko Haram Ya Fasa Kwai
Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar wani tsohon kwamandan ‘yan ta’addan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya ce ya yi watsi da ta’addanci ne sakamakon gano cewa akidar ‘yan ta’addan Boko Haram zamba ce. A cikin bidiyon da PRNigeria ta samu, kasurgumin dan ta’addan ya ce manyan shugabannin kungiyar a koyaushe za su aika su a kashe su ne a fagen daga, tare da yaudarar su cewa aljanna ce za ta zama makomar su idan an kashe su. A cewar Rugurugu, manyan shugabannin Boko Haram ba sa…
Read MoreYunwa: Tsagerun Inyamurai Sun Yi Wa Motar Biredi Tatas A Enugu
Wasu gungun matasa da ake kyautata zaton ‘ya’yan haramtaciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafara, IPOB, sun tare wata motar burodi a Enugu sun sace burodin sannan suka bankawa motar wuta a safiyar ranar Talata. Lamarin ya faru ne a Emene, bayan garin babban birnin Enugu, a ranar da aka umurci mazauna garin su zauna a gida don nuna goyon baya ga Nnamdi Kanu, shugaban Kungiyar tsagerun Inyamuran kamar yadda aka ruwaito. Wani shaidan gani da ido ya ce an kona motar ne a tsohuwar kasuwar Orie Emene Da ya…
Read MoreZa A Farfado Da Ayyukan ‘Yan Sa Kai A Zamfara – Matawalle
Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin jihar za ta farfado da kungiyar hadin guiwa ta tsaro na farar hula ta CJTF wacce aka fi sani da “Yan sa kai” don kawo tallafi ga jami’an tsaron jihar akan ‘yan ta’addan da suka addabi Zamfara. Shugaban kwamitin tsaro da yanke hukunci ga ‘yan bindiga na jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da kamfanin dillacin labarai NAN yayi da shi a ranar Talata. Gwamnatin jihar ta yanke shawarar ne don kawo karshen duk wasu ‘yan ta’adda da…
Read MoreDa Dumi-Dumi: An Kashe Shugaban ISWAP Al- Barnawi
Rahotanni dake shigo mana yanzu daga Jihar Borno na bayyana cewar an kashe shugabann kungiyar ISWAP Abua Musab Al-Barnawi daya daga cikin kungiyoyin dake kai munanan hare hare suna kashe jama’a a yankin Tafkin Chadi. Bayanan dake fitowa daga Najeriyar sun ce an kashe Abu Musab Al-Barnawi ne a karshen watan Agustan da ya gabata kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar. Rahotanni masu karo da juna na nuna cewa sojojin Najeriya ne suka kashe shi, yayin da wasu majiyoyi kuma ke cewa a rikicin cikin gida ya mutu. Ya zuwa wannan…
Read More‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sarkin Bungudu
Wasu ?an bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace sarkin Fulanin Bungudu, da ke jihar Zamfara mai martaba Alhaji Hassan Attahiru. ?an bindigar sun sace sarkin ne kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda ?aya daga cikin ?a?ansa da kuma basaraken masarautar Zannan Bungudu Hon Abdulmalik Zubairu ya tabbatarwa BBC. Bayanai sun ce an kashe ?aya daga cikin jami’in ?an sanda a musayar wutar da ?an bindigar suka yi jami’an tsaron da ke tare da sarkin cikin mota a hanyar Abuja. Babu dai wata sanarwa…
Read MoreBani Da Hutu Sai Naga Bayan ‘Yan Bindiga A Kasar Nan – Shugaban Dakarun Soji
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban dakarun sojin kasa, Janar Faruk Yahaya ya ja kunnen cewa ba zai lamunci uziri daga kwamandojin da ke jagorantar dakarun soji ba a filin daga da kuma yakar matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta ba. Yahaya ya bada wannan wannan jan kunnen a yayin bude wani taro kashi na biyu da na uku na sojin da aka hade a ranar Litinin a birnin tarayya Abuja. Ya ce rundunar da ke karkashinsa za ta cigaba da mayar da hankali tare da…
Read More