‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sarkin Bungudu

Wasu ?an bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace sarkin Fulanin Bungudu, da ke jihar Zamfara mai martaba Alhaji Hassan Attahiru.

?an bindigar sun sace sarkin ne kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda ?aya daga cikin ?a?ansa da kuma basaraken masarautar Zannan Bungudu Hon Abdulmalik Zubairu ya tabbatarwa BBC.

Bayanai sun ce an kashe ?aya daga cikin jami’in ?an sanda a musayar wutar da ?an bindigar suka yi jami’an tsaron da ke tare da sarkin cikin mota a hanyar Abuja.

Babu dai wata sanarwa daga rundunar ?an sandan jihar Kaduna, yankin da al’amarin ya faru.

Sace sarkin wani babban ?alubale ne musamman a daidai lokacin da aka ?auki mataki na toshe layukan sadarwa da hana cin kasuwannin mako domin maganin ?an bindiga masu kai hare-hare- da satar mutane

Related posts

Leave a Comment