Babu Ranar Bude Layukan Sadarwa A Zamfara – Matawalle

Rahotanni daga birnin Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Bello Muhammad, Matawallen Maradun, ya ce babu ranar bu?e layukan sadarwa a jiharsa.

A ranar juma’a wa’adin da gwamnan ya ?iba na bu?e layukan ya cika, kuma a hirarsa da BBC ya ce babu ranar dawo da layukan sadarwar a jihar.

“Dole mu tsawaita don burinmu tabbatar da tsaron al’ummarmu,” in ji gwamna Matawalle.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da jami’an tsaro, kuma makomar tattaunawar ce za ta tantance lokacin da za a bu?e layukan, ko za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Fiye da mako biyu kenan da al’ummar Zamfara ke rayuwa babu hanyoyin sadarwa a fa?in jihar, matakin da hukumomi suka ce sun ?auka domin ?o?arin magance matsalolin ?an bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihar.

Matakin toshe layukan na sadarwa ya shafi yankunan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya kuma yi kira ga jihohin da ke makwabtaka da jiharsa da su ma su ?auki matakin toshe kafofin sadarwa a jihohinsu, inda yake ganin hakan na ?aya daga cikin hanyoyin kawo karshen bala’in ‘yan bindiga a yankin.

Ya ce yana magana da gwamnonin jihohin da ke ma?wabtaka da Zamfara kan ?aukar matakin toshe layuka a jihohinsu.

Matawalle ya ce sun ga alfanun toshe layukan domin a cewarsa toshe hanyoyin sadarwar, shi ya taimaka wajen ku?utar da ?aliban makarantar ?ayar Maradun daga hannun ‘yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata.

Gwamna Matawalle ya yi ikirarin cewa tun toshe hanyoyin sadarwa da aka yi a fa?in Zamfara “babu wani babban abin da ya faru,” yana mai cewa “?an bindiga sun koma suna yi wa wadanda suka sace bulala a madadin ku?in fansa da suka rasa.”

Ya kuma ce azabar yunwa ta sa ?an bindiga suna cin ?anyar ku?ewa saboda sabbin matakan da aka ?auka na toshe hanyoyin sadarwa da hana cin kasuwanni.

“Akwai wani sarki da yake ba ni bayanin cewa ?an ta’adda sun zo bakin gari, ku?ewar da aka shuka a cikin garin duk sun yanke ta, kuma haka nan suke cinta ?anya saboda azaba ta yunwa,” in ji shi.

line

Al’umma a Zamfara sun da?e suna fuskantar hara-haren tare da ?one garuruwansu daga ?an fashi masu ?auke da manyan bindigogi.

Hukumomi da jami’an tsaron sun sha i?irarin cewa suna kokarin ganin an shawo kan matsalar da magance ta baki daya, amma har yanzu ana kai hare-hare da garkuwa da mutane duk da ikirarin gwamnatin Zamfara na yin sulhu da ?an fashin.

Related posts

Leave a Comment